Sin tana fatan ƙungiyar EU za ta gyara ra’ayin kuskure da ta nuna wa Sin

Daga CRI HAUSA

Kakakin tawagar jakadun Sin dake ƙungiyar EU ya yi bayani game da ra’ayin ƙungiyar EU da aka gwada a gun taron kiyaye tsaro na Munich a jiya, inda ya bayyana cewa, ƙasashen yammacin duniya na fuskantar matsaloli, ya kamata su nemi dalilin da ya sa hakan daga kansu. A cikin dukkan manyan matsalolin da suka ko suke faruwa a sassa daban-daban na duniya, ko babu ƙasashen yammacin duniya da suka ko suke tsoma baki ko sa hannu, har ma suka tayar da hankali kai tsaye?

Kakakin ya yi nuni da cewa, ya kamata mu magance bin ra’ayin yaƙin cacar baka wajen tsaron kai a tsakanin ƙasashe daban-daban, kuma kar a bi ra’ayin yaƙin cacar baka a tunanin filsofiya. Wannan ra’ayi ba zai samar da gudummawa ga ƙoƙarin yin mu’amala da haɗin gwiwa a tsakanin al’adu daban-daban ba.

Kakakin ya jaddada cewa, kamar yadda memban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi ya faɗa a gun taron kiyaye tsaro na Munich a jiya cewa, duniya tana fuskantar hadarin nuna kiyayya da juna, ya kamata ƙasa da ƙasa su yi ƙoƙari tare, bai kamata a nuna ƙiyayya ga juna ba, ta hakan za a warware matsalolin dake kasancewa a duniya a halin yanzu, da samun kyakkyawar makoma. Sin da Turai su ne manyan ɓangarori biyu a duniya, tabbas suna da ƙarfi wajen kiyaye zaman lafiya a duniya. Sin tana fatan ɓangaren Turai zai gyara ra’ayin kuskure da yake nunawa Sin, da yin haɗin gwiwa tare da ɓangaren ƙasar Sin don ƙoƙarin gina “wata kyakkyawar duniya” cikin haɗin gwiwa.

Fassarawa: Zainab