Sin tana maraba da ziyarar Jami’ar kare haƙƙin ɗan Adam ta MDD a Xinjiang

Daga CRI HAUSA

Mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin, kana ministan harkokin wajen ƙasar Wang Yi, ya ce, ƙasar Sin tana maraba da zuwan babbar jami’ar kare haƙƙin ɗan adam ta MDD Michelle Bachelet, wacce za ta ziyarci ƙasar, ciki har da yankin Xinjiang.

Wang, yayin da ya halarci taron ƙolin al’amurran tsaro na Munich karo na 58 ta kafar bidiyo, ya yi furucin ne a yayin da ya mayar da martani dangane da batun dake shafar yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na Uygur na ƙasar Sin.

Ya bayyana cewa, Xinjiang wani yankin ne dake kan iyakar wurare masu fuskantar barazanar mayakan ‘yan ta’adda da masu tsattsauran ra’ayi, Wang ya ce, domin tabbatar da tsaron lafiyar al’umma, gwamnatin yankin Xinjiang, tana ɗaukar matakan sauya tunanin masu tsattsauran ra’ayin ta hanyar ilmantarwa, wanda ya yi daidai da manufofin ƙasashen duniya da suka haɗa da Birtaniya, da Faransa, da kuma al’adar ƙasa da ƙasa.

Wadannan matakai sun yi matuƙar tasiri wajen kawar da aƙidun masu tsattsauran ra’ayi, kuma sun samu gagarumin goyon bayan al’ummar yankin Xinjiang, in ji mista Wang, ya ƙara da cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, ba a samu hare haren ta’addanci ba a yankin.

Ya ce, ƙasar Sin tana maraba da baki daga ƙasashen waje su ziyarci yankin Xinjiang domin sanin haƙiƙanin gaskiya kan lamarin.

Ya ƙara da cewa, kafin ɓarkewar annobar COVID-19, yankin Xinjiang ya karɓi bakuncin sama da jami’an gwamnatoci dubu 2, da masu ruwa da tsaki a harkokin addinai, da ma ‘yan jaridu daga ƙasashe sama da 100 da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.

Fassarawa: Ahmad