Sirrin nasarar marubutan Nijar a gasar Hikayata – Nana Aicha Hamissou

“Marubuci hantsi ne leƙa gidan kowa”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Akwai kyakyawar alaƙa da zumunci mai ƙarfi tsakanin marubutan Nijar da Nijeriya kamar yadda marubuciya Nana Aicha Hamissou Abdoulaye ta tabbatar a zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, inda ta bayyana sirrin nasarar da ake ganin marubutan Nijar na samu a shekarun baya bayan nan, musamman a gasar Hikayata ta BBC Hausa. A shekarar 2021 Nana Aicha ta zo mataki na biyu, yayin da a 2022 kuma Amira Souleymane ta samu nasara a mataki na farko. Abin arashin kuma shi ne dukkan su sun fito ne daga gari ɗaya wato Jihar Maraɗi, kuma ƙarƙashin ƙungiyar marubuta ta Madubi. A jerin tattaunawar da jaridar Manhaja ke yi da wasu marubutan Jamhuriyar Nijar, a wannan makon, mun kawo muku hirar mu da Nana Aicha ne.

MANHAJA: Ki gabatar min da kanki.

NANA AICHA: Assalamu Alaikum. Sunana Nana Aicha Hamissou Abdoulaye. Ni malamar makaranta ce, kuma marubuciya daga Jamhuriyar Nijar.

Ki ba mu tarihin rayuwarki a taƙaice.

An haife ni a Unguwar Sabon Gari da ke garin Maraɗi Jamhuriyar Nijar, a shekarar 1994. Na yi karatun addini da na boko daga matakin firamare har zuwa Jami’a duk a garin Maraɗi. A halin yanzu ina matakin digiri ta biyu a Jami’ar Abubakar Ibrahim International University da ke Maraɗi, har’ilayau ni malamar makaranta ce kamar yadda na faɗa a baya, inda nake koyar da darasin Lissafi a wata makarantar sakandire da ke Maraɗi.

Yaushe ki ka fara rubutun labaran adabi, kuma mai ya ja hankalinki?

Na fara rubutu a watan Afrilu na shekarar 2019. Ban taɓa zaton zan zama marubuciya ba, amma yawan karance-karance ne silar tsintar kaina a duniyar marubuta.

Littattafan ki nawa, ba mu labarin wasu a taƙaice?

Na rubuta littafai bakwai ni kaɗai Ýar Aikin Gidana, ‘Da Wa Na Dace?’ ‘Rayuwarmu Ce Haka’, ‘Laila’ ‘Hafsat’, ‘Soyayyar Gaskiya’, sai kuma labarin ‘Wutar Ƙaiƙayi’ da nake kan rubuta shi yanzu haka, da kuma ‘Inuwa Ɗaya’, wanda shi ma ban gama shi ba. Akwai kuma wasu littattafan da muka yi na haɗaka tare da wasu, guda uku: ‘Sai Na ɗauki Fansa’ (mu uku muka rubuta shi), sai ‘Hannu Ɗaya’, Ba Ya Ɗaukar Jinka’ (mu goma tare da marubutan Kainuwa), sannan sai littafin ‘Da Jininsa A Jikina’ (shi ma yana shirin fita tare da zaratan marubuta guda tara ni ce ta goman su).

Na kuma rubuta gajerun labarai fiye da 15, akwai ‘A Sanadin Mijinta’, ‘Wani Jinkiri’, ‘Kuskuren Da Na Tafka’, ‘Ramin Mugunta’, ‘Na Yi Nadama’, ‘Tun A Duniya’, ‘Hoton Mijina’, ‘Wata Rayuwa’, ‘Rai Da Ƙaddara’, da kuma ‘Butulci’ wanda na samu nasara da shi a Gasar Hikayata ta BBC Hausa.

Waɗanne irin labarai ne ki ka fi sha’awar rubutawa?

Marubuci hantsi ne leƙa gidan kowa. Don haka ba ni da wani keɓaɓɓan jigo da nake rubutu a kansa, duk inda ta faɗi sha ne a wajena.

Yaya dangantakar ki da marubutan adabi na Nijeriya?

Ina ji da su, ina alfahari da su, ina yi masu fatan alheri. Nakan ce su ɗin, ‘yan’uwana ne waɗanda akwai ɓoyayyiyar ƙauna tsakanin mu, rubutu ne silar bayyanata. Dangantakarmu mai ƙarfi ce saboda wasu har iyayenmu sun san da zaman su.

Yaya ki ka iya gane ƙa’idojin rubutun Hausa na Ingilishin Nijeriya da irin naku na Nijar?

Marubuci mutum ne mai bincike kafin tsoma alƙalami cikin tawada zuwa bisa takarda. Har’ilayau abin da ya shige duhu a kan nemi masana ko kuma a karanta maƙalu domin amfanuwa a karan kai da kuma rubuta wa al’umma. A taƙaice dai ina fahimtar su ta hanyar bincike da karantar rubutun manyan masana.

Kin taɓa zuwa Nijeriya don wata harkar marubuta ko zumunci?

Na sha zuwa Nijeriya domin sada zumunci. Na taɓa zuwa sau ɗaya domin karrama ni a gasar BBC Hikayata ta 2021. Ina kuma sa ran sake shiga domin wata karramawar kasancewar ina ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasara a gasar Ɗan Giwa.

Bani labarin rayuwar marubuta labaran Hausa a Nijar?

Akwai marubuta da makaranta labaran Hausa da dama a Jamhuriyar Nijar. Kuma suna rayuwar zumunci a tsakanin su gwanin birgewa, suna ƙoƙarin kiyaye ƙa’idojin rubutu, duk da Hausar shiyyarmu ba ta yi kama da daidaitacciyar Hausa ba.

Ba ni labarin Ƙungiyar Madubi ta marubutan adabi, kuma me ya bambanta ta da sauran ƙungiyoyin marubuta na Jamhuriyar Nijar?

Ƙungiyar Madubi kamar sauran ƙungiyoyin marubuta ce. Muna da mambobi da kuma shugabanni kamar kowacce ƙungiya. Kuma ƙungiya ce ta qasa mai rijista da gwamnati, don haka muna da mambobi kusan daga kowacce jiha a faɗin Ƙasar Nijar. Shugabar ƙungiyar Madubi ta yanzu ita ce Amira Souley, gwarzuwar Gasar Hikayata ta BBC Hausa na shekarar 2022.

Wacce gudunmawa Ƙungiyar Madubi ta ke bayarwa ga cigaban harkokin rubutun adabi a Nijar?

AlhamduLillah! Zuwa yanzu ƙungiyar ta fara tallafa wa marubutanta, ta hanyar koyar da su abubuwan da za su sa su inganta rubutunsu, kuma ita shugaba ta ɗaukar mana malamai suna koyar da mu darussa da za mu sake inganta rubutunmu da kiyaye ƙa’idojin rubutu. Muna fatan nan gaba kaɗan ƙungiyar ta yi suna da ɗaukaka ta ban mamaki, ba iya Ƙasar Nijar ba har ƙasashen ƙetare sunan ta ya zagaye duniya.

Sunanki ya fara ɗaukaka ne a lokacin da ki ka samu nasarar zama ta biyu a Gasar Hikayata ta BBC Hausa a 2021. Yaya ki ka ji a wancan lokacin?

A ranar da aka sanar da ni ina cikin gwaraza uku da suka yi nasara a gasar BBC, ban yi bacci ba tsabar farincikin da na tsinci kaina ciki.

A karo na biyu ýar Nijar daga Jihar Maraɗi ta zama ta farko na gasar Hikayata ta 2022, menene sirrin wannan nasara ta ýan Nijar?

Sirrin nasarar kawai zan ce daga Ubangiji ne. Domin ko a bara da muka kasance cikin 25 ɗin farko ni da ita mun ci buri da fatan mu zama cikin gwaraza uku na farko matuƙar akwai alheri a nasarar tamu. Dayake rabon ta kasance ta farko ne sai Ubangiji Ya jinkirta mata samu nasarar har sai a shekarar da ta gabata. Ka ga kuwa zan iya cewa sirrin nasarar mu ni da ita rabo ne daga Allah, da kuma sa’a wacce bayan tana tafe da jajircewa.

Wanne ƙawance gwarazan Gasar Hikayata ke shirin ƙullawa don tallafa wa sauran marubuta?

Duk abin da zai taimaka masu muna ƙoƙarin taimakawa da ɗan abin da muka sani duk da mu ɗin ma har yanzu rarrafe muke yi, wasu ne suke yi mana tata tata. Muna da buri mu tallafa masu daga abin da muka tsinta wurin manyanmu.

A ƙarshen shekarar da ta gabata an shirya liyafa a Maraɗi domin taya shugabar Ƙungiyar Madubi kuma Gwarzuwa Amira Souley murna, yaya ku ka ji da yadda marubuta daga Najeriya suke baku goyon baya?

Tun lokacin da suka sanar da mu za su halarci taron na shiga cikin farinciki ni da sauran ‘yan’uwana, musamman ma sauran da ba mu taɓa tozali da su ba a zahiri, a ranar da suka taho na matsu su iso. Na shiga farinciki sosai da muka yi gana da su, musamman da suka yanke uzurorin su don halartar taronmu. Har kawo yanzu ina jin daɗin zuwan su, ina yi masu addu’ar fatan alheri da samun ladan zumunci.

Su wanene suke tallafa muku wajen koya muku yadda za ku inganta rubutun ku, daga gida Nijar da Najeriya?

Gaskiya a shekarun baya muna rubutu ne kara zube, saboda rashin sanin ƙa’idojin rubutu da kuma su kansu dabarun rubutun. Amma yanzu AlhamduLillah! Bayan tsintar kanmu a zaurukan marubuta daban daban a mahanjar WhatsApp, muka fara fahimtar abubuwa a hankali. A halin yanzu cikin yardar Allah muna ganewa har mukan taimaka wa kanmu wa junanmu, inda mutum bai gane ba ya yi magana a fahimtar da shi, in wani ya samo abin ƙaruwa yakan turo mu ƙaru gabaɗaya. Har’ilayau akwai malamin da aka ɗauko yana yi mana darasin ƙa’idojin rubutu, idan ya gama kuma wani daban zai ɗora mana darasin Dabarun Rubutu.

Gaya min aminanki da ku ke gogayya a harkar rubutun adabi?

Akwai ‘yar’uwata Rahma Sabo Usman, da ƙawancen marubuta mata shida da muke yi wa laƙabi da 6stars Indeed’ waɗanda suka haɗa da Hauwa’u Salisu, Farida Sweery, Maryam Nasir, Jannat M. Nasir, Aisha Sani Abdullahi, sannan kuma akwai Rukkaya Ibrahim Sokoto, Fatima Abdullahi Galadima, da Aisha Fulani.

Wacce shawara za ki so ki bayar ga jagororin harkar rubutun adabi a Nijar domin koyi da na Najeriya?

Shawarata su tallafa mana, su dinga shirya mana gasa duk shekara kamar yadda ake wasannin kokowa da kuma sauran wasannin motsa jiki.

Shin kina da burin nan gaba ke ma ki buga littafi?

Ina da wannan burin, in sha Allahu, nan ba da daɗewa ba.

Bangon littafin ‘Tun A Duniya’

Wacce shawara za ki bai wa sauran matasan marubuta da ku ke mu’amala tare a online?

Madalla. Ina son in yi kira ga ‘yan’uwana marubuta da su ji tsoron Allah domin duk abin da muka rubuta za a tambaye mu shi a gobe ƙiyama. Don haka mu rubuta abin da zai amfani al’umma, ko bayan ranmu al’umma ta yi amfani da shi, ana saka mana albarka idan an karanta.

Sannan su yi rubutu don faɗakarwa kar su yi don neman ɗaukaka, domin ɗaukaka ta ɗan lokaci ce amma saƙon da za su isar zai amfani al’umma har duniya ta naɗe.

Bayan dara akwai wata cacar, bayan abubuwan da na zayyano ya kamata su yi wasu abubuwa da za su ƙara ingata masu rubutu kamar, yawaita karance-karance, kar su yi wa rubutu karatun nishaɗi, su yi masa karatun nazari, su nazarce shi bi-da-bi su fahimci yadda ake rubutu domin su ƙaru. Su dinga tambayar masana, kafin su saki labari, su yi tambayar ga wanda ke da sani game da wani ɓangare na labarin. Idan labarin malami ne su yi tambayar malamai, in likita ne su ga likita, in lauya ne su nemi lauya, haka in harkar ‘yan sanda ce sai su nemi ɗan sanda don su nemi sani. Har ila yau yana da kyau su nemi littattafan sanin ƙa’idojin rubutu, nahawu da karin magana, kuma su dinga karanta muƙalu na adabi.

Sannan yana da muhimmanci marubuta su cire girman kai su nemi masana, kar su ji haushi don an yi masu gyara, ko kuma an yi masu dariya, kar su bari gwiwarsu ta yi sanyi su kasa miƙewa. Su sani duk wani wanda ya miqe tsaye da ƙafafuwansa sai da ya fara koyon tafiya, don haka duk wanda ka gani yau sai ya biyo ta jiya. Kafin su fara sakin labari su tura wa wanda ya fi su sani ya duba masu, ya fitar masu da kurakurai.

Su yi haƙuri kar su ce a lokacin da suka turo lokacin suke muradi, su ba shi lokaci domin gyara ko mutum da kansa ya yi rubutu akwai wahala balle rubutun wani da kake ɗaukar lokaci ba ka fahimci wani abu ba. Kar su yarda a yi masu gyara guda har sau uku. Ke nan matuqar aka yi gyara na farko ba su fahimta ba su buɗe baki su kwantar da kai su sanar da wanda ya yi masu gyara inda ba su gane ba, bayan ya gama yi masu bayani su yi masa tambayar qa’idar abin da ba su ba gane ba. Ina ga hakan zai sa su yi saurin fahimta.

Kada su kuskura su ce lokaci guda za su yi gasa da wane ko wance, ma’ana kada su ce so nake ko ta halin ƙaƙa sai na zama wane. A’a lokaci ne da kansa zai mayar da su fiye da wanda suke son koya. Domin tsalle ɗaya ake yi a faɗa rijiya amma akan yi dubu ba tare da an fito ba. Su raba kansu da shiga zaurukan yanar gizo barkatai masu cakuɗe da mata da maza matuƙar ba tattaunawar ilmi ake yi a ciki ba.

Mata su ji tsoron Allah su daina hirar da ba ta da kai tare da wasu maza, marubuta ko akasin haka. Haka maza ma kar su nemi dole sai sun yi hira da wasu matan matuƙar ba tataunawar ilmi ba ce, ita ma kar a wuce gona da iri. Kar a zo wurin biɗar ƙiba a samo rama, ana faɗakawar da al’umma a ɗayan gefe, gefe guda kuwa ana sava wa Ubangiji.

Wani zunibi da muke ɗaukar shi ƙarami ya fi saurin illata mu. Don haka matan aure har ma da ‘yan’mata sabbin marubuta su kiyaye haƙƙolin ubangiji, in sun yi haka za su rabauta duniya da lahira.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwar ki?

Wani jinkiri alheri ne.

Mun gode.

Ni ma na gode.