Siyasar ɗan jarida

Kamar dai yadda muka sani ne cewa, halin mutum jarinsa. Ban fifita ’yan jaridu ko marubuta a kan sauran al’ummu ba. Amma a zahiri mai aiki na jarida idan zai yi siyasa zai yi jama’a.

Kar mu manta marigayi Kakakin Nufe Sam Nda Isaih wanda ya rasu a 2021 kuma kamin ya rasu Mr Nda ya taɓa yunƙuri na neman takara ta shugabancin ƙasa wanda a kai zaɓe na fitar da gwani a ranar 11/12/2014, inda ya zamo na biyar amma har haka Mista Nda ya ci gaba da aikin jagoranta da shugabantar kamfanin Jaridar Leadership.

A gefe guda Margayi Dr Alh Bashir Osman Tofa wanda ya rasu a wannan shekara ta 2022 marubuci kuma ɗan siyasa wanda ya yi takara a Jam’iyyar NRC a matsayin mai neman shugaban ƙasa.

Yanzu kuma ga alamu Shugaban Jaridar Blueprint mai fitar da Manhaja, Alhaji Muhammad Idris a makon watan fabrairu ya nuna buƙatar neman zamowa magajin gwamnan Jiharsu ta Neja. An ce himma ba ta ga raggo. Muna fatan alkhairi gare shi, domin mutumin kirki ne.

Daga Mukhtar Ibrahim katsina  Saulawa. 07066434519, 08080140820.