Siyasar Bauchi: Rikicin Dogara da Bala ya ƙazance

*…Bayan kai wa sarakunan jihar farmaki
*Gwamnan ya maka tsohon kakakin a kotu

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed da abokin adawar siyasarsa a Bauchi kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai ta Nijeriya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, sun dulmiya cikin kogin shari’a, don lalubo bakin zaren wanda ya fi yin tasiri a tsakaninsu a cikin al’ummar Sayawa da ke jihar ta Bauchi.

Gwamna Bala dai ya rattaba abokin adawar tasa ne tare da wasu abokan tarayyarsa guda 28 a Babbar Kotun Jihar Bauchi bisa zarge-zarge 11, waɗanda suke da nasaba da aikata muggan laifuka na tashe-tashen hankali.

Sanata Bala, wanda shi ne Babban Jami’in Tsaro na Jihar Bauchi, a cikin ƙarar, ya yi zargin kashe da ɓarnata dukiyoyi a gabanin bikin tunawa da wani gwarzo mai kishin al’ummarsa ta Sayawa, Marigayi Baba Peter Gonto, wanda aka buɗe a garin Ɓogoro, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Ɓogoro a cikin jihar kwanakin baya.

Gwamnan, a cikin takardar koken sammaci wacce magatakardar babban kotun ta Bauchi ya sanya hannu ranar 5 ga Janairu, 2022, ya zayyana koke-koke guda 11 waɗanda ya ke so Yakubu Dogara a matsayin babban mai kariya da abokan tarayyarsa guda 28 su amsa a gaban kotun.

A cikin takardar ƙarar mai lamba BA/01/22, gwamnan ya zargi masu kariyar ne da laifin haɗin kai tare da yi wa mutane raunuka da zummar wargaza tsarin gudanar da bikin tunawa da gwarzon, wanda aka shirya yin sa a garin Ɓogoro a ranakun 30 da 31 ga Disamba da suka gabata.

Koke-koken tuhumomin su ne kamar haka: “dangane da sashi na 98 (1) da (2); sashi 100 (b) da 103 (b) na gudanar da shari’a kan munanan laifuka na jihar Bauchi na shekara ta 2018. Ana tuhumar masu kariyar ne, waɗanda Hon. Yakubu Dogara yake jagoranci da suka haɗa da Air Commodore Ishaku Komo mai ritaya mazaunin garin Kaduna da Rev. Markus Musa mazaunin garin Tafawa Ɓalewa.

Sauran sun haɗa da Peter Emmanuel mazaunin garin Tafawa Ɓalewa, Ga’Allah Daniel, mazaunin garin Tafawa Ɓalewa, Iliya Emmanuel, mazaunin garin Tafawa Ɓalewa da sauransu cewar, ku a ranar ko ma’abutan ranakun 29, 30 ko 31 ga watan Disamba ta shekarar 2021 kuka haɗa kai da amincewa ku haddasa ko aikata ba daidai ba.

“Har wa yau, dangane da sassan dokoki da aka ambata a sama, waɗanda ake zargin, ana tuhumar su da haɗin kai a tsakanin su, da kuma waɗansu da suka arce, da harzuƙa matasa a garuruwan Tafawa Ɓalewa da Bogoro domin su tayar da hankulan jama’a, ta hanyar ƙona gidajen jama’a, tare hanyoyi, dayin farmaki wa baƙin da aka gayyata bikin shekara ta 21, Ƙaddamar da Littafi da Gidauniya na tunawa da Gwarzo, Mai kishi marigayi Baba Peter Gonto a garin Bogoro.

Katoɓarar, kamar yadda tuhume-tuhumen suka zayyana, sun kai ga lalata da ƙona kayayyaki da aka daje dandalin bikin da su, don haka an aikata laifi wanda ya yi banbaraƙwai da sashi 96 wanda ya tanadi hukunci a sashi na 97 na kundin dokokin jihar Bauchi.

“A rana ko kusanci da ranakun 29, 30 ko 31 ga watan Disamba na shekara ta 2021 kuka amince da yi ko sanadiyyar yin abinda yayi saɓani da doka, kuka yi haɗin baki a tsakanin ku, da waɗansu da suka arce, kuka aikata laifi na amfani da wuta, tare da ƙona gidajen jama’a a garuruwan Tafawa Ɓalewa da Ɓogoro, yayin gudanar da bikin tunawa da ƙaddamar da littafi kan tarihin rayuwar marigayi Baba Peter Gonto a garin Bogoro, haɗi da lalata da ƙona kayayyaki da aka daje wajen gudanar da bikin da su, wanda yin hakan laifi ne a ƙarƙashin sashi na 97 na kundin dokokin jihar Bauchi.”

Tuhume-tuhumen dai ba su ambaci yawan mutane da ake yin zargin an kashe ba a yayin aikata katoɓarar, ko yawan gidaje da aka ƙona ba, amma rahotanni da ba a gaskata da su ba, sun yi zargin kashe mutane shida, haɗi da ƙona gidaje, motoci da dukiyoyin jama’a, da aka yi shaguɓen tamɓararrun matasa sun aikata a lokacin tashin-tashinar.

Idan za a iya tunawa, Sarakunan Bauchi da na Dass, Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da Alhaji Usman Bilyaminu Othman, aka kai wa jerin gwanon motocinsu farmaki a kan hanyarsu ta zuwa garin Ɓogoro, domin amsa gayyata da aka yi masu na zuwa taron, inda aka raunana wasu motoci da ke cikin tawagar.

Masu lura da harkokin siyasar jihar na kallon lamarin a matsayin yadda siyasar Babban Zaven 2023 ke ci gaba da dagulewa a jihar ne, musamman tsakanin Bala da Dogara.

Ba a dai sanya ranar fara sauraron wannan ƙara ba, wacce Gwamna Bala Mohammed ya shigar su a gaban kotu.