Siyasar kuɗi ba alheri ba ce ga Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Hada-hadar siyasa na cigaba da kankama gadan-gadan a Nijeriya. Kawo yanzu dai akasarin jam’iyyun siyasar ƙasar nan sun kammala gudanar da zavukan su na fitar da gwanayen ’yan takarar da za su tsaya ƙarƙashin tutar su, don neman muƙamai a matakai daban-daban, daga kan gwamnoni, majalisun dokoki na jihohi, zuwa Majalisar Ƙasa a ɓangaren Majalisar Wakilai ta Tarayya da Majalisar Dattawa, da Shugaban Ƙasa. Manyan jam’iyyun APC da PDP dai har yanzu su ne suka fi jan hankalin jama’a, yayin da aka samu farfaɗowar wasu ƙananan jam’iyyun da jama’a suke kallon su a matsayin tudun talakawa, inda ‘yan siyasa masu aƙida da masu ƙaramin ƙarfi ke ganin a nan ne za su iya fakewa don gwada nasu farin jinin da neman goyon bayan talakawa ‘yan uwansu. Jam’iyyun siyasa irin su NNPP wacce madugun aƙidar siyasar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yake jagoranta, da jam’iyyun PRP, SDP, ADC, da LP waɗanda su ma nasu tauraron ke haskawa na samun nasu tagomashin.

A yayin da manyan jam’iyyun siyasar ƙasar nan, suka kammala zaɓen fitar da ‘yan takararsu, wanda ya yi ta jan hankalin jama’a, wani ɓangare da ya fi janyo muhawara a tsakanin ‘yan ƙasa shi ne yadda aka gudanar da siyasar deliget, wato irin kuɗaɗen da aka riƙa amfani da su wajen sayen wakilan jam’iyyu masu fitar da ɗan takara, wanda a tarihin siyasar ƙasar nan ba a taɓa ganin haka ba. Ƙiri-ƙiri a bainar jama’a haka aka riƙa cinikin deliget ana ba da maƙudan kuɗaɗe, domin neman goyon bayan deliget. Abin da ya riƙa tsorata ƙananan ‘yan siyasa, ya sanya wasu shiga neman bashi, wasu kuma suka haƙura ma da takarar ganin ba za su iya kashe maƙudan kuɗaɗen da ake buƙata ba.

Batun kuɗaɗen sayen fom ɗin neman tsayawa takara shi ma ya ja hankalin ‘yan Nijeriya sosai, saboda tsadar da kuɗin sayen fom ɗin ya yi, musamman na jam’iyyar APC mai mulki, a matakin shugaban ƙasa, wanda ya kai har Naira miliyan ɗari abu ne da ya zo wa ‘yan Nijeriya a bazata kuma ya jawo muhawara mai zafi a kafafen watsa labarai da wuraren tarukan jama’a, kan batun dacewa ko rashin dacewar tsawwala kuɗin neman shiga takara.

Alamu na nuna cewa, lallai siyasar Nijeriya ta shiga wani sabon babi, inda sai masu hannu da shuni ne kawai za su iya samun damar murza zaren siyasa, babu sauran duba cancanta, halaye nagari, aƙida mai kyau, gogewa ko kuma ƙwarewar tafiyar da mulki. Iya kuɗin ka ne iya shagalinka! Jari hujja tsantsa!! Amma anya kuwa hakan alheri ne ga ƙasar nan?

A yayin da miliyoyin matasan ƙasar nan ke fama da zaman kashe wando babu ayyukan yi, ƙalubalen taɓarɓarewar tsaro ke ci gaba da mayar da ƙasar nan baya, ‘yan makaranta da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandire da jami’o’i ke zaune a gida tsawon watanni saboda yajin aikin malamai, bisa buƙatun da suka gabatar wa gwamnatin tarayya na ɗaukar matakan inganta jami’o’i da harkokin ilimi. Sai gashi ana ta facaka da biliyoyin Naira ana, ana sayen ra’ayin masu fitar da ‘yan takara, waɗanda su kuma idanun su suka rufe kan abin da za su samu, ba tunanin cancanta ko makomar ƙasar ce a gaban su ba.

Babu shakka akwai abin tsoratarwa da fargaba kan yadda za a shiga yaƙin neman zaɓe, yayin da ake tunkarar Babban Zaɓen 2023, inda ‘yan takarar da jam’iyyun siyasa suka tantance kuma suka fitar za su bar deliget su juya wajen talakawa da su kuma za su fita su kaɗa ƙuri’unsu ga ‘yan takarar da deliget suka zaɓar musu. Ko sun dace ko ba su dace ba. Ko da ya ke ba yanzu aka fara ba, dama an daɗe ana samun wasu ‘yan Nijeriya da ke sayar da ’yancinsu wajen neman a basu wani abu kafin su yi zave, don haka yanzu ganin irin facaka da wadaƙar da aka riƙa yi wajen sayen ƙuri’un deliget, babu mamaki idan an samu ƙaruwar waɗanda za su riqa rububin neman a biya su kafin zavi wani ɗan takara!

Haka su ma malaman addini waɗanda dama suke rayuwar hannu baka hannu ƙwarya, su da iyalan su, yanzu ne za su fitar da tasu maitar a fili (malamai su gafarce ni), domin kuwa babu mamaki idan an samu wasu masu rauni a cikin su sun wasa wuƙaƙensu domin jiran tagomashi daga wajen ‘yan siyasa da za su riqa ziyartarsu akai-akai, don neman goyon bayan su da na almajiran su, da sauran jama’ar gari, kasancewar yanzu siyasa a Nijeriya ta zama kamar wani ɓangare na addini. Kowanne ɗan siyasa zai duba wanne abin zai kama ya yi yaƙin neman zave da shi don ‘yan uwansa musulmi ko kirista su bashi goyon baya. Duk kuwa da kasancewar lokacin da ya ke bin deliget yana watsa kuɗi bai yi la’akari da wanene Musulmi ko Kirista a cikin su ba.

Su ma sarakuna iyayen ƙasa da ake sa ran za su zama ‘yan ba ruwan mu, a zavukan baya an yi ta zarge-zargen tsoma bakin su cikin hidimar siyasa wanda har ya jawo tarzoma da cin mutunci ga wasu da aka fi ambatar sunayen su tare da zarge-zarge da dama. Don haka a wannan lokaci da siyasa ta zama hajar kasuwanci da rabon kuɗaɗe, nauyi ne a kan sarakuna da malamai su tsare mutuncin rawunansu da hulunan su, su faɗakar da mabiyansu da ‘yan siyasar su kansu, muhimmancin yin abin da ya dace, da kawar da kai daga sayar da ’yancinsu, domin fitar da nagari ko waɗanda muke ganin suna da dama-dama, don su kawo wa ‘yan ƙasa sauyi daga halin koma bayan da ake ciki.

Kamar yadda xaya daga cikin ‘yan takarar neman shugabancin ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyyar APC a zaɓen fitar da gwanin da ba a daɗe da kammalawa ba, wato Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha, ya faɗa ne a jawabin sa na neman goyon bayan deliget, ya ƙalubalanci ‘yan Arewa su tambayi sauran abokan takarar sa wanne cigaba suka kawo wa yankin a baya? Mu ma yanzu haka tambayar da ya kamata mu yi wa ‘yan takarar da za su ziyarce mu nan gaba kaɗan kenan, wanne abu ku ka yi mana da ku ke ganin idan muka zaɓe ku za ku ruvanya mana shi? Babu tabbas ga abin da wani ɗan siyasa zai zo ya ce zai yi, idan har a baya ba a ga alamun shi mai yi ɗin ba ne.

Ba ma buƙatar ‘yan jari hujja waɗanda kansu kawai da dukiyarsu suka sani. Waɗanda ke ganin sun ciyo bashi ne ko sun zuba jari ne, don su samu riba, ba don su yi wa ƙasa aiki ko su kawo wa talaka canji a rayuwarsa ba. Kuma ba wai muna ƙyamar manyan ‘yan siyasa masu hannu da shuni ko ‘yan kasuwa ba ne, amma muna son ganin waɗanda za su yi amfani da ƙwarewar su a harkokin kasuwanci, da sha’anin mulki, don kawo wa qasa cigaba.

Shugabanci nagari ba lallai sai ga talakan ɗan siyasa ko mai kishin addini ba, hasali ma yawancin su ba ƙwararrun masu tafiyar da mulki ba ne. Amma mai kishin talakawa, mai son cigaba ko wanene, zai iya kawo wa ƙasa sauyi, ko da ba yankin ku ɗaya ba ko ba addinin ku zaya ba.

Mu guji siyasar addini, mu guji siyasar kuɗi, babu alheri a cikinta. Mu nemi ɗan takara na gari daga kowacce jam’iyya ya ke, matuƙar mun gamsu da ƙwarewarsa da nagartarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *