Siyasarmu a yau

Assalamu alaikum. Barkanmu da har haka, da fatan kowa yana cikin ƙoshin lafiya. Allah ya albarkaci jaridar Blueprint Manhaja, Amin.

Gabanin zuwan zaɓe, waye zai zama angon Nijeriya a 2023?

Shekaru 23 kenan, da fara mulkin dimukraɗiyya a Nijeriyya, an yi shugabanni daban-daban, a kuma yi jami’iyyua na siyasa daban-daban, kamar irin su; Jam’iyar PDP, wanda ita ce ta fara mulkin ƙasar nan a tsari ma dimukraɗiyya, sai kuma APC, wanda ita ce ke kan mulki yanzu haka bayan da PDP ta yi shekara 16 a mulki, yanzu kuwa APC ne ke kan mulki.

Cif Obasanjo ne ya mulki ƙasar daga shekara ta 1999 zuwa 2007, tare da Alhaji Atiku Abubakar. Sai kuma daga 2007 zuwa 2015, Umaru Musa Yar Aduwa da Godluck Ebele Jonathan sunyi mulki na shekaru 2, sai kuma Allah ya ɗauki ran Alhaji Umaru Yar Adua, yayin da Jonathan da Alhaji. Namadi Sambo suka cigaba da mulki har zuwa shekara ta 2015 ɗin.

A halin yanzu, tun daga shekara ta 2015 ɗin, zuwa yanzu, wanda ana sa ran shekara mai zuwa wa’adin mulkinsa zai ƙare, Muhammadu Buhari ne da Ferfesa Osinbajo ne ke mulkin ƙasar.

Ana daf da shigowa Babbar zaɓe, tuni dai jijiyoyi, tare da jini sun harzuƙa, wajen neman kujerar ta shugaban ƙasa. Ana ta tunanin waye zai haye waye kuma zai sha ƙasa.

Sama da mutane 10 ne ake tsammanin sun sayi tikitin neman kujerar, daga kuma jam’iyu daban-daban, ciki akwai jami’iyya ta APC mai mulki a yanzu, da kuma jam’iyya ta hamayya PDP mai neman kujerar, ba iya anan ba akwai wasu sabbin jam’iyya da suka haɗa NNPP mai alamin kayar marmari da kuma PRP da sauran su.

Wutar yaƙin na ƙara ci, yayin da ko wanne ɗan takatar na da salo da ya ke da shi wajen jan hankalin al’umma. Mu ɗauki jam’iyya mai ci a yanzu, APC. Bisa ga dukkan alamu dai, kallo da kuma tsarin da yarjejeniya tsakani ’yan jam’iyya na nuna cewa yankin kudu ne ke da alhakin fitar ɗan takara. A yanzu haka, akwai Rotimi Amechi, da kuma Omahi, da Gwamnan Ikiti sai kuma Jagaban Asiwaju Ahmed Bola Tinubu. Duk da cewa a yankin Arewa ta tsakiya akwai Gwamnan Kogi mai ci, Alhaji Yahaya Bello, amman wannan wasu na ganin kamar yana sharan fage ne.

A jam’iyya ta hamayya kuma, PDP, akwai Gwamnan Bauchi mai ci yanzu, Barista Mohammed Bala (Kauran Bauchi), sai tsohon Shugaban majilisar dattawa, Abubkar Bokola Saraki, Gwamnan Sokoto Ahaji Aminu Waziri Tambuwal, da kuma Nelson Wike na Jihar Ribas da kuma tsohon mataikamin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar. Jam’iyya hamayyar ta rabu kusan gida uku. Rukunin farko shi ne ɓangaren su Tambuwal da Saraki da Kaura, rukuni na 2 sune masu cewa ayi karɓa-karɓa a baiwa Ɗan kudu sune ɓangaren Wike, sai kuma ɓangaren daddy kawai, waton ɓangaren Alhaji Atiku.

A wata sabuwar jami’yya kuma, na NNPP. Sabuwar jam’iyya ce, wadda duka-duka bata kai shekara 2 da samar da ita ba. Akwai tsohon Gwamnan Kano, kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa Dr. Rabi’u Musa kwankwaso, wanda shi ne ɗan takarar shugabancin ƙasar a jam’iyyar.
Waɗannan jam’iyyun 3, sune manya waɗanda kallo ya koma gare su. Kuma a cikin jam’iyyun, APC, bisa ga dukkan alamu jagaban ne ke kan gaba, haka kuka PDP, Atiku ne ke kan gaba kamar yadda NNPP kuma kwankwaso ne akan gaba.

Duk wani tsari na tasirin cigaba, ko samar da abinda babu, ko gogayya da wasu manyan ƙasashe Jagaban wannan mai sauki ne a wurin shi. Kamar yadda ya ce, “yana son ƙasar ta Nijeriya ta zama tana gogayya da manyan ƙasashe a duniya ba iya Afirka ba.

Wasu na ganin da wannan hasashen nema kwankwaso ɗin ya cilla zuwa sabon jam’iyya ɗan ya gwada sa’ar sa. Kwankwason ya ce, ƙasa babu zama lafiya, baka isa kaje nan da can ba, kuma wannan Gwamnatin ta yaudare al’umma saboda shima yana son ya gwada don ya kawo ƙarshen taɓarɓarewar tsaro. Kano na ɗaya da cikin jihohin da suka fi kowace jiha zaman lafiya. A shekara ta 2012 zuwa 2013, wani yunƙuri na kutsen Boko Haram ya so ya taso a Kano, lokacin Kwankwaso ne akan mulki, abin bai wani tasiri ba, an kawo ƙarshen lamarin. Wanda tasirin wannan ne yasa har yau babu masu garkuwa da mutane a Kano.

Sannan kwankwaso, ya kawo  cigaba na faɗaɗa jihar, kamar samar da gadan sama da titin ƙasa, sai kuma batu na ruwan sha da sauran su. Wannan ne ma yasa Kwankwaso yana ganin yana so ya gwada sa’arsa ya gani ko zai kai labari.

Alhaji Atiku Abubakar, wanda tshohon mataimakin Shugaban ƙasa ne, kuma ya yi takara a inuwar PDP a shekara ta 2019. Ya ce, “ƙasa babu tsaro, kuma yunwa ta addabi mutane”. A jawabin da ya yi na bayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar, ya ce, babban aikin da ke gaban shi shi ne samar da zaman lafiya tsakanin ‘yan ƙasa”.

Batun Ibo baya son Hausawa, ko Hausawa basa son ‘yan kuɗi, ko Yarabawa ba su son wani ƙabila ba nasu ba. Ya ce, “wannan abin na ci masa tuwo a kwarya, daman Nijeriya ba haka ta ke ba”. Ya ce zai kawo ƙarshen wannan rabe-raben, sannan tabbatar da ƙasar ta zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

Atiku, wanda ƙungiyar kamfen nasa ma masa kirari da Dadi, ya taka muhimmiyar rawa wajen hana wanzuwar ƙungiyar Boko Haram a wasu jihohi a arewa maso gabashin Nijeriya. Musamman a Adamawa, lokacin da Boko Haram suka kwace wasu ƙananan Hukumomi a Borno, irin su Bama, Dambuwa, da kuma Gwoza, ba da jimawa ba a shakara ta 2014 suka zarce zuwa yankunan arewacin Jihar Adamawa, Madagali, Michika da Mubi, Hong da Song, a daidai lokacin da suke yunƙurin zarce wa zuwa cikin Yola, Atiku ya yi rawan azo a gani, ya sa aka kore su, wanda har zuwa yau zaman lafiya na cigaba da wanzuwa.

Wannan rawa da Atiku ya taka a lokacin, yana daga cikin muhimman batutuwa da suka rusa Gwamnatin Jonathan, sannan ya kawo nasarar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Dukkan ‘yan takarar nan 3, da Tinubu, da Atiku, da Kwankwaso, suna da tasiri, musamman ma idan aka yi duba zuwa ƙoƙarin da suka yi a shekara ta 2015, wanda hakan ya sa Buhari ya lashe zaɓe. Kuma ko wannensu na da jami’a, ma’ana mabiya masu yawa. To amman waye zai yi nasara a mulkin, waye zai zama angon Nijeriya a cikin su.

Sannan wane irin shugaba Nijeriya ke buƙata?

In sha Allahu, mako mai zuwa zamu ɗaura daga inda muka tsaya. Allah ya zaɓa mana shugaba mafi alkhairi. Ameen.
Wassalam.

Saƙo daga Mohammed Albarno. O8034400338, [email protected]