Soja ya harbe abokin aikinsa sannan ya kashe kansa

Rundunar Sojin Nijeriya ta fara bincike kan wani soja kan zargin harbe abokan aikinsa har lahira sannan ya kashe kansa a sansanin sojoji da ke Rabbah a Jihar Sakkwato.

Kakakin rundunar, Birigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayyana cewa ya zuwa yanzu ba a tantance haqiqanin abin da ya faru ba, amma dai sojan ya harbe kansa bayan hallaka abokin aikin nasa.

Nwachukwu ya kara da cewa Babban Hafsan Runduna ta 8 (GOC) kuma Kwamandan hundunar haɗin gwiwa ta Operation Northwest, Hadarin Daji, Manjo Janar Godwin Mutkut, da wasu manyan hafsoshi sun ziyarci wajen da lamarin ya afku.

A cewarsa, GOC ya jajanta wa sojojin da suka rasa abokan aikinsu a sansanin.

“Ya buƙace su da su zama masu kula da junansu kuma su ba da rahoton duk wani rikici da ke faruwa a tsakaninsu don gudun sake faruwar irin hakan.

“Ya ƙara musu kwarin gwiwa da su kwantar da hankalinsu tare da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

“Hukumomin Sojojin Nijeriya sun damu matuƙa game da wannan lamari mai ban mamaki kuma sun kafa kwamitin bincike don bankaɗo abin da ya faru.

“Ana hasashen cewa sakamakon binciken zai taimaka wajen daƙile irin wannan munanan lamari a nan gaba,” in ji Nwachukwu.