Sojoji sun bindige ɓarawon akwatin zaɓe a Kogi

Daag MAHDI M. MUHAMMAD

Sojojin Nijeriya sun bindige wani ɓarawon akwatin zaɓe da ba a san ko wane ne ba a hanyar Ogege, sashin zaɓe na Odaba a gundumar Dekina da ke Jihar Kogi.

An tattaro cewa, masu kaɗa ƙuri’a a yankin sun tsere daga filin kaɗa ƙuri’a sakamakon ayyukan ’yan bangar siyasa da suka zo da yawa domin lalata kayayyakin zaɓe.

’Yan barandan da suka bayyana ɗauke da adduna da bindigu sun yi awon gaba da akwatunan zaɓe tare da karya kujeru tare da tarwatsa masu kaɗa ƙuri’a.

Bayan harin, an soke zaɓen mazaɓu bakwai na mazaɓar Kogi ta Gabas, inda aka soke rumfunan zaɓe biyu a Anyigba da ke yankin Ƙaramar Hukumar Dekina, da sauran biyar a Ƙaramar hukumar Omala ta jihar Kogi.

A wani labarin kuma, an ce an kashe mutane biyu a unguwar Ndi Agwu da ke Abam a Ƙaramar Hukumar Arochukwu a jihar Abiya.

An bayyana cewa, an samu asarar rayuka a yayin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokokin ƙasar da aka gudanar a yau.

Rahotanni sun ce ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe mai suna Samuel Arunsi Eze an ce wani ɗan siyasa da aka fi sani da Daniel Mgba ya sare kansa.

A cewar wani shaidar gani da ido, an kuma kashe ɗaya daga cikin waɗanda ke da hannu a kisan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *