Sojoji sun ceto ma’aikatan jinƙai daga hannu ISWAP

Sojoji sun ceto biyu daga cikin ma’aikatan jinƙai ukun da mayaƙan ISWAP suka yi garkuwa da su a Borno.

Waɗanda lamarin ya shafa ma’aikatan ƙungiyar nan ce ta Family Health International (FHI360).

Majiyarmu ta tattaro cewar a ranar Laraba aka kuɓutar da ma’aikatan.

An yi garkuwa da ma’aikatan ne a masaukin baƙin ƙungiyar da ke ƙauyen Fotoko kusa da Gamborou Ngala, Jihar Borno kwanan baya.

Majiyar News Point Nigeria ta ce har yazu da wasu mutum uku a hannun mayaƙan.

Sai dai tun bayan sace ma’aikatan babu wata sanarwa a hukumance a kan hakan, walau daga ɓangaren sosjoji ko ƙungiyar da suke yi wa aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *