Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Rundunar Sojojin Nijeriya a ranar Laraba, ta tabbatar da murƙushe haramtattun matatun mai a Imo da Delta, tare da kama wasu litar man da aka tace ba bisa ƙa’ida ba.
Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa a ranar Laraba a Abuja.
Nwachukwu ya ce, dakarun sojojin na 343 Artillery Regiment, a ranar Litinin ɗin da ta gabata, sun fatattaki wani sansanin ɓarayin mai da ke unguwar Obokofia a Imo yayin da suke gudanar da aikin satar mai.
Ya ƙara da cewa, sojojin sun kuma kwato injinan fanfo guda biyu, injinan samar da wutar lantarki guda uku, tiyo ɗaya da kuma akwatin kayan aiki da ake amfani da su wajen kutse cikin bututun mai.
Nwachukwu ya ce, sojojin, yayin da suke aiki da sahihan bayanai, a ranar Talata, sun kama wani kwale-kwalen katako cike da ganga 110 na fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba da aka ɓoye a cikin rafukan Egbema West a ƙaramar hukumar Ohaji Egbema ta Imo.
“Dakarun sun kama wasu motoci biyu ɗauke da ganga 18 na fetur da aka tace ba bisa ƙa’ida ba a yankin.
“Ana kira ga jama’a da su kai rahoton duk wani aiki da ake zargi na yin zagon ƙasa ko aikata laifuka ga hukumomin tsaro don inganta ayyukan da ake cigaba da yi na daƙile zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasar,” in ji shi.
A cewarsa, “Dakarun Bataliya ta 3 ma a ranar Litinin ɗin da ta gabata, sun yi artabu da wani haramtaccen wurin tace man da ke ɗauke da tanderun girki uku da tafkunan ruwa shida a unguwar Enokora da ke qaramar hukumar Burutu ta Delta.”