Sojoji sun gasa wa mayaƙan Boko Haram/ISWAP gyaɗa a hannu a Wulgo

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga babban ofishin sojojin Nijeriya da ke Abuja, na nuni da cewa sojojin rundunar ‘Operation Haɗin Kai’ da ke aikin haɗin gwiwa da sojojin Kamaru a yankin Arewa-maso-gabas, sun kakkaɓe wasu mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin Wulgo.

Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na facebook mai ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, rundunar ta ce a ranar Litinin da ta gabata sojojin suka samu wannan nasarar a kan ‘yan ta’addan inda suka yi fatafata da su.

Sanarwar ta ce ‘yan bindigar sun cimma ajalinsu ne a daidai lokacin da suka yi yinƙurin kai hari a sansanin sojojin inda sojoji suka farga tare da daƙile yinƙurin nasu.

Ofishin rundunar ya ce sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram uku yayin artabun tare da ƙwace bindigogi ƙirar AK 47 guda uku da alburusai guda 50.

A wata mai kama da wannan, wasu mayaƙan ISWAP/Boko Haram su huɗu sun cimma ajalinsu duk a rana guda kusa da sansanin Bataliya ta 151.

Bayanan rundunar sun ce ‘yan bindigar sun ƙone ƙurmus ta yadda ba a iya gane mutum sakamakon arangamar da suka yi da sojoji.

Babban Ofishin Rundunar ya ce sojoji na ci gaba da sintirin aiki a yankin domin ƙarasa kakkaɓe ‘yan bindigar da ke yankin.

Tuni Shugaban Sojojin Nijeriya, Lieutenant General Faruk Yahaya, ya yi jinjina da yabo ga dakarun da suka damu wannan nasarar. Tare da kira a gare su da su matsai ƙaimi wajen daƙile ‘yan bindigar da harkokinsu a yankin baki ɗayansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *