Sojoji sun kama babbar mota ɗauke da alburusai da aka yi nufin kai su Anambra

Daga BASHIR ISAH

Sojojin Nijeriya sun kama wata babbar motar ɗaukar kaya ɗauke da alburusai da nufin kai su Jihar Anambra.

Rundunar sojin ta ce dakarun Bataliya ta 192 da ke yankin Dibishan 81 su ne suka kama motar ranar Asabar a daidai lokacin da aka yi amfani da ita wajen yin fasakwaurin alburusan.

Rundunar ta ce an gano motar ce mai lamba ENU 697 XY a hanyar Ajilete-Owode cikin Ƙaramar Hukumar Yewa ta Arewa, Jihar Ogun, ɗauke da katan 720 na alburusai.

Ga ƙarin hotuna:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *