Sojoji sun karɓe mulki a Gabon

Sojojin ƙasar Gabon sun sanar da ƙwace iko daga gwamnati mai ci tare da rushe sakamakon zaɓen da aka bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe.

Kafin sanarwar sojojin, bayanai sun ce an shafe tsawon sa’o’i ana jin ƙarar harbin bindiga a sassan Libreville babban birnin ƙasar kodayake babu tabbacin ko musayar wuta ce ko kuma kawai sojojin na harbin iska ne.

Cikin jawabin kai tsayen da suka yi ta gidan talabijin ɗin ƙasar da safiyar Laraba, sojojin sun sanar da rushe dukkanin sassan gwamnati ciki har da majalisun dokoki da kuma kotun kundin tsarin mulki.

A cewar Sojan wanda ba a kai ga bayyana sunansa ba, ba su gamsu da yadda zaɓen shugaban ƙasar ya gudana ba, kuma za su kawo ƙarshen tarnaƙin da ƙasar ke fuskanta.

Dambarwa ta kaure a Gabon ne tun bayan kammala zaɓen shugaban ƙasar, wanda ya kai ga katse Intanet da kuma sanya dokar hana fita, lamarin da ɓangaren adawa ya kira da yunƙurin tafka maguɗi.

Lamarin ya tsananta ne bayan hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da shugaba Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar duk da yadda ɓangaren adawa ke iƙirarin samun rinjayen ƙuri’u.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *