Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 109 da kama 81 a mako ɗaya – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Juma’a ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta ce jami’anta sun yi nasarar kashe ƴan ta’adda 109 da kama wasu 81 acikin mako guda a wurare mabanbanta.

Ta kuma ce jami’an nata sun kama wasu mutane shida da hannu a satar mai tare da ceto mutane 43 da aka yi garkuwa da su.

A cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa Labarai na hedikwatar, Manjo-Janar Edward Buba ya fitar, ya ce a Kudu maso Kudu, sojojin sun daƙile satar ɗanyen mai da wasu ɓarayi suka yi yunƙurin yi da adadin kuɗinsa ya kai Naira miliyan 618.75.

Ya ce jami’an tsaron za su cigaba da ƙoƙarin daƙile ayyukan ƴan ta’adda a dukkanin sassan Nijeriya.

Ya ƙara da cewa jami’an sun ƙwato bindigogi guda 21 da kuma alburusai guda 124.

Har’ilayau, jami’an sun ƙwato motoci 4 da babura 6 da salula guda huɗu da ɗanyen mai da ya kai lita 631,709 da aka sace da lita 3,140 na gas da aka tace ta haramtacciyar hanya da kuma fetur lita 2,250 sauran su.