Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dakarun Operation Fansan Yanma sun yi nasarar kashe wani da ake zargin mai safarar makamai ne ga ‘yan’ta’adda a garin Nasarar Burkullu dake Ƙaramar hukumar Bukkuyum mai suna Alhajin Gas Wanda ɗan asalin garin ne.
Rohotanni daga yankin na nuni da cewar an samu Nasarar hallaka Alhajin Gas ne lokacin da yake ƙoƙarin tserewa bayan yayi artabu da jami’an tsaro.
Hakazalika wakilin mu ya ruwaito cewar dakarun sojin sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga huɗu, sun kama ɗaya a lokacin samamen da suka kai a yankin na Nasarawar Burkullu bayan samun bayanan sirri cewar Alhajin Gas ya ɗauko makamai a motarshi domin ya basu.
Wanda ake zargin Alhajin Gas an Kuma same shi da makaman da yake da nufin isarwa ga ‘yan bindiga.
Ganau ya shedawa wakilin mu cewar, lamarin dai ya faru ne a wani samame da aka kai cikin dare a garin Nasarawa Burkullu a Jihar Zamfara, inda jami’an tsaro da ke aiki da bayanan sirri suka kama wanda ake zargin yana safarar makamai daga garin Anka.
“Da ganin sojojin, wanda ake zargin ya yi yunƙurin tserewa amma cikin gaggawa suka bude mashi wuta ya mutu nan take”.
“Binciken farko da aka yi ya tabbatar da cewa yana jigilar bindigogi da alburusai ne zuwa ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a yankin, inda ƙungiyoyin ke kukan cewa sun samu ƙarancin albarussai da makamai yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi a kansu”. A cewar ɗaya daga cikin mazaunin garin.
Kawo ya zuwa yanzu, babu wata sanarwa da rundunar Operation Fansan Yamma ta fitar dangane da lamarin a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.