Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 73 a cikin makonni biyu – Hedikwatar Tsaro

Daga UMAR M. GOMBE

Babban Ofishin Tsaro da ke Abuja ya ce an samu kashe mayaƙan Boko Haram guda 73 a tsakanin makonni biyu a yankin Arewa-maso-gabas.

Daraktan yaɗa labarai na rundunar tsaro na ƙasa, Bernard Onyeuko, shi ne ya bayyana haka ran Alhamis, yana mai cewa rundunar shirin Operation Haɗin Kai ce ta samu wannan gagarumar nasarar.

Jami’in ya ƙara da cewa sojojin sun ƙwato makamai masu tarin yawa daga sassa daban-daban a wajen ‘yan ta’addan

Ya ce a ranar 27 na Yunin da ya gabata, sojojin sun karɓi wasu ‘yan Boko Haram su 55 da suka yi saranda suka miƙa wuya ga sojoji a Darajemel da ke Barno, mutanen sun haɗa da maza da mata har da ƙananan yara.

Onyeuko ya ce makaman da suka ƙwato a wajen ‘yan ta’addan sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda 44, PKT guda biyu, bindigar harɓo jirgin sama guda 7, alburusai, kayan abinci, barguna da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *