Dakarun rundunar ‘Operation FANSAN YANMA’ sun yi nasarar kashe fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Kachallah Hassan Nabamamu, wanda aka fi sani da Hassan Ɗantawaye, bayan da ya yi yunƙurin tserewa tare da kwance ɗamarar wani soja a Gusau dake Jihar Zamfara.
Nabamamu, wanda ya daɗe yana ta’addanci a yankin Tsafe da Mada, yazo hannu ne yayin wani sumame da sojoji suka kai dabar sa a Mada dake ƙaramar hukumar Tsafe a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Nabamamu yayi ƙoƙarin tserewa yayin da Sojoji suka ɗauko shi a safiyar ranar 28 ga watan Fabrairu daga Tsafe zuwa Gusau, inda hakan yayi sanadiyyar kashe shi.
Ya kasance ɗaya daga cikin jagororin ‘yan bindiga da ake fargaba a Zamfara sakamakon yadda yake miyagun ayyukan ta’addanci da suka haɗa da garkuwa da mutane da karɓar kuɗin fansa, da kai munanan hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaro.
Tsawon shekaru, ’yan ƙungiyarsa sun ɗauki alhakin kai hare-hare marasa adadi a garuruwan da ke kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, ciki har da harin da akai a garuruwan Makera, Chediya, Agama Lafiya, Singawa, Yalwa, da Rekebu.
Haka kuma ya sha kallafawa al’ummar Tsafe biyan haraji wanda ya tilasta wa mazauna yankin biyan makudan kuɗaɗe da yi musu barazanar kisa.
Hakazalika, sojojin sun kai harin kwanton ɓauna tare da kashe wasu manyan kwamandojin ‘yan bindiga guda biyu, Na-Allah da Dogo Basulluɓe.
Dakarun rundunar Operation FANSAN YANMA na cigaba da ƙara ƙaimi a sassan jihohin Zamfara, Katsina, Sokoto, da Kebbi a makonnin da suka gabata tare da kai hari ta sama da ƙasa wanda ya kai ga kawar da wasu manyan jagororin ‘yan bindiga da kuma ceto wasu mutane da dama da aka yi garkuwa da su.