Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 28, sun kuɓutar da mutum 82 a mako guda

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya a ranar Alhamis ta ce dakarunta sun kama jimillar masu aikata laifuka 114 da suka haɗa da ’yan ta’adda 92, da ’yan bindiga 6, da kuma masu satar mai 7 a cikin makon da ya gabata a yayin farmakin da suka kai kan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da sauran masu aikata laifuka a faɗin ƙasar.

Sojojin sun kuma ceto sama da mutum 82 da aka yi garkuwa da su daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su tare da kashe ‘yan ta’adda sama da 28 a cikin wannan lokaci.

Manjo Janar Edward Buba, Darakta mai kula da harkokin yaɗa labarai na tsaro ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wani taron mako na mako-mako kan nasarorin da sojojin suka samu a wurare daban-daban na ƙasar.

Janar Buba ya yi nuni da cewa, a cikin wannan lokaci da aka mayar da hankali a kai, sojoji tare da sauran jami’an tsaro sun gudanar da ayyukan kwanton-vauna, kai samame, aikin sintiri, da kuma kai farmaki ta sama, inda aka yi nasarar kawar da ’yan ta’adda, da ceto wasu da aka yi garkuwa da su.

Daga cikin ’yan ta’addan da aka kawar sun haɗa da 14 a Arewa maso Yamma, 7 a Arewa maso Gabas, da 3 kowanne a Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu.

Har ila yau, an kama wasu masu aikata laifuka 14 a Arewa maso Yamma, 18 a Kudu maso Gabas, 23 a Kudu maso Kudu, 11 a Arewa ta Tsakiya da 5 a shiyyar Arewa maso Gabas yayin da aka kuvutar da mutane 51 da suka haɗa da iyalan ‘yan ta’adda a Arewa maso Gabas, 26 a Arewa maso Yamma, 3 a Arewa ta Tsakiya da 2 a shiyyar Kudu maso Gabas.

Manjo Janar Buba ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci sojojin sun kwato tarin makamai sama da 108 da alburusai 564.

A cewarsa, saboda tsananin ƙarfin tasirin da sojojin suka yi akan ‘yan ta’adda, sama da ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP 72 ne suka miƙa wuya ga dakarunsu a wurare daban-daban a shiyyar Arewa maso Gabas.

Daraktan ya bayyana cewa, an miƙa dukkan ’yan ta’addan da suka miƙa wuya, da aka ceto fararen hula, waɗanda aka kama da kuma kayayyakin da aka kwato, an miƙa su ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike mai zurfi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *