Sojojin Najeriya sun yi nasarar kuɓutar da aƙalla mutane 98 daga hannun yan ta’adda, cikinsu harda yarinya ɗaya daga cikin yan matan Chibok da akai garkuwa dasu shekerun baya.
Anyi wannan nasarar ne a wani atisayen soja mai taken ” Operation Lake Sanity II” wanda cigaba ne daga atisayen baya mai taken “Operation Hadin kai”
Wasu bayanai na sirri da Zagazola, ƙwararre a harkar tsaro ya samu ya nuna yar Chibok ɗin da aka ceto itace mai lamba ta 64 a cikin jerin sunayen yan matan Chibok ɗin da akai garkuwa dasu.