Sojoji sun lalata maɓuya da kasuwar Boko Haram/ISWAP a Borno

Daga BASHIR ISAH

Hedikwatar Runduhar Sojojin Nijeriya ta ce, dakarunta na ‘401 Special Force Brigade’ tare da haɗin gwiwar ’19 Brigade’ a Baga sun yi nasarar lalata maɓuyar Boko Haram/ISWAP sa’ilin da suke sintiri a yankunan Kauwa da Gudumbali a jihar Borno a ranar Talatar da ta gabata.

Rundunar ta bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na facebook a ranar Laraba.

Ta ce dakarunta sun samu lalata maɓuyar mayaƙan ne yayin da suke aikin tsaftace yankunan da lamarin ya shafafa daga harkokin ‘yan ta’adda, tare da cewa za ta yi ƙarin bayani kan lamarin nan gaba.

Kazalika, rundunar ta ce ko a wannan Larabar sai da dakarunta na ’25 Task Force Brigade’ da ke Damboa, jihar Borno, suka tayar da wata kasuwar dare a yankin Gumsuri wadda aka ce mallakar BokoHaram/ISWAP ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *