Sojoji sun ragargaji ‘yan Boko Haram a Barno

Daga WAKILINMU

Mayaƙan Boko Haram a Jihar Barno sun kwashi kashinsu a hannu bayan da Dakarun ‘Operation Lafiya Dole’ wanda a yanzu suke kan aiwatar da ‘Operation Tura Takaibango’ a yankunan Dikwa da Gulumba Gana, tare da haɗin gwiwar sojojin sama suka fatattake su

Daraktan Hulɗa a Jama’a na sojojin, Brigadier General Mohammed Yerima shi ne ya bayyana haka.

General Yerima ya ce ‘yan ta’addan sun yi amfani da wasu motocin yaƙi ne wajen kai wa yankunan da lamarin ya shafa hari a Lahadin da ta gabata, kuma a daidai lokacin da jama’a ke shirye-shiryen buɗa bakin azumin wannan rana.

Ya ci gaba da cewa bayan da dakarun suka yi galaba a zangon farko na harin ‘yan Boko Haram ɗin, sai suka dare suka bai wa mayaƙan sama sarari inda su kuma suka yi luguden wuta kan ‘yan ta’addan da motocinsu.

A sanyin safiyar Litinin da ta gabata dakarun suka far wa ‘yan ta’addan inda suka samu galaba a kansu tare da ƙwato yankin Dikwa.

A cewar Yerima, ‘yan Boko Haram sun ji jiki yayin artabun da aka yi wanda ya yi sanadiyar kashe wasunsu da dama da kuma lalata musu kayayyakin faɗa.

Bayanan rundunar sojijin sun nuna a halin da ake ciki dakaratunta na ci gaba da sintiri a garin Dikwa da kewaye domin tantance ɓarnar da aka yi wa ‘yan Boko Haram ɗin.

Haka nan, rundunar ta ce Shugaban Rundunar Sojoji, Lieutenant General Ibrahim Attahiru, ya jinjina wa dakarun bisa wannan gagarumar nasarar da suka samu. Tare da bada tabbacin cewa Sojojin Nijeriya ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen ci gaba da bai wa yankin Arewa-maso-gabas tsaron da ake buƙata.