Daga BELLO A. BABAJI
Gidauniyar Harkar Jaridar Binciken ƙwaf (FIJ) ta tabbatar da hakan a ranar Juma’a ta kafafen sada zumunta.
FIJ ta ce sojojin sun sako Fisayo Soyombo ne bayan ƙorafe-ƙorafe da al’umma suka ta yi game da tsare shi.
A yanzu ta na ƙoƙarin bincike game halin da ya ke ciki bayan fitowarsa daga hannun sojojin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar sojojin reshen, Laftanal Kanal Danjuma Danjuma ya tabbatar da kama ɗan jaridar, ya na mai cewa sun kama shi a wani haramtaccen wajen jido mai.