Sojoji sun tsinci ɗalibai uku da aka yi garkuwa da su a Kaduna

An gano ƙarin ɗalibai uku na makarantar Bethel Baptist Secondary school da ke Kaduna waɗanda aka yi garkuwa da su lokutan baya.

Ɗaliban da lamarin ya shafa wanda baki ɗayansu maza ne, sojoji ne suka gano su a dajin Kankumi a yankin ƙaramar hukumar Chikun.

Bayanan da MANHAJA ta kalato sun nuna ɗaliban tserewa suka yi daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su tun farko.

An ce bayan da aka sace su a makarantarsu ranar 5 ga Yuli, ɗaliban sun sake faɗawa hannun wani gungun ɓarayin bayan da suka kuɓuta daga hannun ɓarayin farko inda suka rasa hanya a cikin daji.

An bayyana cewa gungun ɓarayin na biyu da ɗaliban suka faɗa hannunsu sai da iyayen yara suka biya fansa kafin ɓarayin suka sake su a nan dajin da sojojin suka tsince su.

Ana sa ran bayan kammala duba ɗaliban a miƙa su ga hukumar makarantarsu domin yin abin da ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *