Sojoji sun yi juyin mulki a ƙasar Gabon

Sun soke zaɓen Shugaban Ƙasa Ali Bango na. Gabon wadda iyalan gidan suka shafe shekara 53 suna mulki lamarin da ya da suka kasance daga cikin shugabannin ƙasa da suka jima suna jan zaren su a karagar mulki a duniya.

Soja sun yi juyin mulki tare da soke sakamakon zaɓe mai cike da maguɗi wanda aka jima ana zargin iyalan gidan Ali Bango da aikatawa, lamarin da ya sa ƙasar ke fuskantar ƙorafin siyasa da maguzin zaɓe.

Libraville babban Birnin ƙasar Gabon na ƙunshe da ’yan ƙasar waje da ke gudanar da kasuwancin katako da sauran harkoki, kuma akwai ’yan Nijeriya masu yawa a can saboda ƙasar Gabon ke kan gaba a duniya kan harkar kasuwancin katako.

Bayan haka ’yan ƙasar na cin moriyar duk wani tallafin gwamnati wanda ya sa suke rayuwa cikin jin daɗi kamar ƙasashen Larabawa, Amma duk da haka ƙorafin siyasa ya sa an yi juyin Mulki a ƙasar don haka ya kamata ’yan siyasar Nijeriya su yi hattara su nisanci son zuciya su lura da mawuyacin halin da mutane suka shiga na tsananin yunwa da talauci da rashin aikin yi da tashin hankali su magance lamarin, idan sun ƙi ji ba za su ƙi gani ba.

Da fatan Allah ya ceci bayinsa a ruwan sanyi.

Daga Muazu Hardawa Edita Jaridar Alheri Bauchi Dandalkura radio reporter. 08062333065.