Sojojin Isra’ila sun kai farmaki a yammacin gaɓar kogin Jordan

Sojojin Isra’ila sun harbe wani Bafalasɗine har lahira tare da raunata aƙalla wasu mutum huɗu, biyu kuma na cikin mummunan hali a birnin Nablus da ke yammacin gavar kogin Jordan, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu da ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta sanar.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce an harbe wani mutum kafin wayewar garin jiya Alhamis, yayin da mayaƙan Falasɗinawa suka ce suna artabu da sojojin Isra’ila da mazauna yankin Nablus.

Aƙalla Falasɗinawa huɗu ne suka samu raunuka sakamakon harbin bindiga, biyu kuma na cikin mawuyacin hali, inji ƙungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasɗinu a wani abin da ta bayyana da arangama da sojojin Isra’ila a gabashin Nablus, wani birni da ke arewacin gaɓar yammacin kogin Jordan wanda ya kasance cibiyar gwagwarmayar Falasɗinawa game da mamayar Isra’ila.

Bataliyar Nablus na dakarun al-Quds Brigades, reshe masu dauke da makamai, ta ce mambobinta suna yaƙar sojojin mamaya da ƙungiyoyin da suka kai farmaki a yankin kabarin Yusuf, tana mai nuni da wani wurin ibada a birnin, inda aka sha fama da arangama tsakanin Falasɗinawa da sojojin Isra’ila.

Sojojin Isra’ila ba su amsa buƙatar jin ta bakinsu ba kan sabon kisan gilla da aka yi wa wani Bafalasdine, wanda ya biyo bayan farmakin da sojojin Ƙasar Isra’ila suka kai a farkon watan nan a sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin da ke da nisan kilomita 41, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasɗinawa 12, da jikkata wasu kimanin 100, tare da yin varna mai yawa a kan ababen more rayuwa na farar hula, wanda hakan ya tilastawa dubban mutane tserewa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, sojan Isra’ila ɗaya ya mutu a harin da aka kai yankin Jenin.

A cikin watan Fabrairu ne sojojin Isra’ila suka kashe Falasɗinawa 11 tare da raunata fiye da mutane 80 a wani samame da suka kai Nablus wanda ya haɗa da sojoji 150 da motoci masu sulke da dama. Wannan farmakin ya biyo bayan ƙasa da wata guda bayan an kashe Falasɗinawa 10 a wani hari makamancin haka da aka kai sansanin ‘yan gudun hijira na Jenin.

Tashe-tashen hankula a Yammacin Kogin Jordan sun ƙara taɓarɓarewa cikin watanni 15 da suka gabata, tare da ƙaruwar hare-haren da Isra’ila ke kaiwa, da kuma hare-haren da Falasɗinawa ke kaiwa kan tituna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *