Sojojin Jamhuriyar Kongo sun ƙwace yankin da ‘yan tawayen M23 suka mamaye

Jami’an Sojin Jamhuriyyar Demokraɗiyyar Congo sun sanar da sake ƙwace yankin da ya kubce daga hannunsu yayin farmakin ‘yan tawaye a ƙarshen makon nan wanda kuma ya hallaka dakaru da tarin fararen hula a gabashin ƙasar.

Ma’aikatar tsaron ƙasar ta zargi mayaƙan ‘yan tawayen M23 da ƙaddamar da farmakin kan sansanin sojinta da ke yankin Rutshuru a gabashin ƙasar. 

Kakakin Sojin ƙasar Janar Sylvain Ekenge ya ce dakarunsu yanzu haka sun bi sahun mayaƙan ‘yan tawayen inda suke ci gaba da gwabza yaƙi don fatattakarsu a ƙoƙarin murƙushe barazanarsu.

Ko a jiya, Hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutane 11,000 suka tsallaka Uganda daga gabashin Jamhuriyar Demokraɗiyyar Congo don gujewa rikicin da yankin ke ci gaba da fuskanta.

Kakakin hukumar Shabia Mantoo ta ce galibin waɗanda ke cikin ‘yan gudun hijrar mata ne da ƙananan yara bayan tsanantar arangama tsakanin dakarun Sojin ƙasar da ƙungiyar ‘yan bindigar arewacin Kivu.

A cewar hukumar, yanzu haka Uganda na ƙoƙarin zama qasa mafi ɗauke da ‘yan gudun hijira a Afrika bayan wasu masu neman mafaka dubu 8 da suka isa yankin Bunagana da kuma wasu dubu 3 a Kibawa.