Sojojin juyin mulki a Nijar sun naɗa ministoci duk da gargaɗin ECOWAS

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Masu juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun kafa sabuwar gwamnati duk da umarnin Ƙungiyar Ƙaya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS).

Shugabannin sojojin sun sanar da sabbin ministoci 21 a wata doka da aka karanta a gidan talabijin na ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne gabanin wani taron gaggawa da shugabannin ƙungiyar ECOWAS ta Yammacin Afirka suka yi kan juyin mulkin da aka yi a Nijar, bayan da hafsoshin sojin ƙasar suka bijirewa wa’adin da aka ba su na dawo da zavavven shugaban ƙasar.

Janar Abdourahamane Tchiani ne ya sanar da sabuwar gwamnatin Nijar, wanda ya karanta wata sanarwa a daren Laraba.

Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine ne zai jagoranci gwamnatin mai wakilai 21, tare da janar-janar a sabuwar majalisar mulkin sojan da ke jagorantar ma’aikatun tsaro da na cikin gida.

Naɗin sabon firaminista da jagororin juyin mulkin suka yi a farkon wannan mako ya nuna alamar fara miqa mulki ga sabuwar gwamnati.

Makonni biyu bayan juyin mulkin da ya hamvarar da Mohamed Bazoum, Ƙungiyar ECOWAS ta ce tana neman hanyar diflomasiyya amma ba ta yanke hukuncin yin amfani da ƙarfin soji wajen warware rikicin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *