Sojojin Najeriya sun gama da Malam Baƙo, magajin Shugaban ISWAP ɗin da suka kashe, Al-Barnawiy

Daga AMINA YUSUF ALI

Mai ba wa Shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari shawara a kan sha’anin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya sanar da mutuwar Malam Baƙo, magajin tsohon shugaban wannan ƙungiyar ta’addancin mai haɗari ta ISWAP, Abu Musab Al-Barnawiy.

Munguno ya yi wannan bayani ne, a lokacin da yake jawabi ga wakilai daga majalisar dokoki, a yayin taron ganawa tsakanin shugaban ƙasa da shugabannin tsaron ƙasar nan, ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Abuja.

A dai taron wanda shugaban ƙasa Buhari ya jagoranta, an yo waiwaye game da mutuwar tsohon shugaban na ISWAP Albarnawiy wanda Janar Lucky Irabor ya tabbatar da faruwar kashe shi da sojojin Najeriya suka yi. Idan za mu iya tunawa, a ranar 14 ga watan Octabar shekarar 2021 da muke ciki, shi Janar Irabo ya ƙara jaddada mutuwar Al-Barnawiy.

A halin yanzu kuma, shi ma sabon shugaban ISWAP, Malam Baƙo ya bi sahun tsohon shugaban da ya gaji kujerarsa inda shi ma kwanansa ya ƙare.

Abin dubawa a nan shi ne, a gaskiya hukumomn tsaron ƙasarnan sun yi aikin a zo a yaba. Domin a cikin abinda bai fi wata guda ba, sun kawar da shugabancin ƙungiyar nan mai hatsari ta ISWAP, wato ta hanyar kisan Abu Musab Al-Barnawiy.

Sannan kuma, kwanaki biyu kacal da suka wuce ƙaya daga cikin shugabannin majalisar Shura ta ISWAP, Malam Baƙo shi ma an kawar da shi. A inda aka bar ‘yan ƙungiyar a rikicin samar da shugabanci. Domin abu ne mai matuƙar wuya a wajensa saboda su suna da matsala ta yarda da juna da zargin juna da sauran abubuwa.

Ko ba a faɗa ba, alamomi sun nuna cewa, ƙungiyar ISWAP da sauran takwarorinta suna amsar matsin lamba daga ayyukan hukumomin tsaron ƙasar nan suke yi a Arewacinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *