Sojojin Nijeriya na iya murƙushe ‘yan ta’adda – Gwamna Sule

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce sojojin Nijeriya na da ƙarfin da za su iya lalata duk wasu masu ɗauke da makamai da ke dagula zaman lafiyar al’umma.

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata a yayin gudanar da ayyukan jin daɗin jama’a na Afirka ta Yamma na 2023 na rundunar sojojin Nijeriya ta IV a ƙaramar hukumar Doma ta jihar.

Gwamnan ya yaba da kokarin sojoji da sauran jami’an tsaro a yaƙin da suke yi da garkuwa da mutane, ‘yan fashi da sauran matsalolin tsaro a ƙasar nan.

Gwamnan ya kuma yaba wa jami’an runduna ta musamman wajen magance masu aikata laifuka a jihar.

A wajen bikin, Sule ya yaba wa rundunar bisa yadda ta ci gaba da gudanar da taron jin daɗin jama’a na shekara-shekara, da nufin haɗa kan jami’ai da iyalansu domin ƙarfafa dankon zumuncin da ke tsakanin ƙabilu daban-daban na sojoji.

Gwamnan ya ci gaba da cewa taron wata dama ce ga hafsoshi da sojoji na cuɗanya da baje kolin al’adunsu.

Ya ƙara da cewa hakan na nuni ne ga ƙudurin sojojin Nijeriya na samar da hanyar da za ta sada zumunci da sauran sojoji da iyalai.

Gwamnan, don haka ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnatin jihar.

“Rundunar sojojin na musamman ta IV, wani ɓangare ne na musamman na sojojin Nijeriya, waɗanda ke da alhakin ayyukan jiragen sama, yaƙi da ta’addanci, tsaron cikin gida da ƙasashen waje da yaƙi da ba a saba ba da dai sauransu.

Gwamna Sule ya ƙara da cewa, “A matsayinku na masu kishin ƙasa, wannan gwamnati za ta ci gaba da tallafawa kokarin jami’an tsaron mu ta hanyar samar da motocin tsaro domin sa ido da sauran tallafi domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan ƙasar.”