Sojojin Nijeriya sun kashe alƙalin alƙalan ‘yan ta’adda

Daga BASHIR ISAH

A cigba da yaƙi da ‘yan ta’adda da suke yi a faɗin ƙasar nan, sojojin Nijeriya sun taki nasara a wani samame da suka kai wa mayaƙan ISWAP inda suka kashe wasu kwamandojinsu ciki har da alƙalin alƙalan ‘yan ta’addan.

Kwamandojin da suka rasa rayukan a wannan karon sun haɗa da Musa Amir Jaish da Mahd Maluma (alƙalin alƙalan ISWAP) Abu-Ubaida da Abu-Hamza da kuma Abu-Nura Umarun Leni.

Bayanan da MANHAJA ta tattaro sun nuna matse ƙaimin da sujojin suka yi a bakin aiki ne ke ci gaba da bai wa sojojin damar samun nasara a kan ‘yan bindigar.

Da ma dai a baya Zagazola ya ankarar cewa mayaƙan Boko Haram/ISWAP sun yi dandazo a dajin LCB/Sambisa inda suka yi shirin kai wa sojoji farmaki a Baga da Malam Fatori a yankunan Abadam da Marte da Mafa kuma kudancin Borno da Yobe.

Majiyoyi sun ce lallai nasarar da sojoji ke samu a kan ‘yan ta’addan a bayyane take, tare da cewa nan da ‘yan kwanaki za a ji kyakkyawan labari game da nasarar da sojojin ke ci gaba da samu.

A cewar majiyoyin ‘yan ta’addan sun shirya kai harin ne a matsayin ramuwa game da kakkaɓar da rudunar Operation Haɗin Kai ta yi wa mayaƙansu a yankin Bukar Mairam.

Tun bayan mallakar jirgin yaƙi samfurin A-29 Super Tucano da sojojin saman Nijeriya suka yi, hakan ya taimaka wa sojojin wajen ci gaba da fatattakar ‘yan ta’addan yadda ya kamata.

Ganin bayan ‘yan ta’adda da ta’adanci a Nijeriya shi ne alwashin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi da yake burin cikawa kafin ƙarewar wa’adin mulkinsa.