Sojojin Nijeriya sun musanta taimakawa wajen kashe mutane a Filato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja

Rundunar sojin Nijeriya, ƙarƙashin tawagar ‘Operation Safe Haven’, ta musanta zargin da ake yi ma ta na rura wutar rashin tsaro a jihar Filato.

Rundunar ta kuma bayyana cewa, adadin sojoji uku da jami’i guda ’yan bindiga sun kashe su a tsakanin watan Janairun bana zuwa, wanda hakan bai tsayar aikin wanzar da zaman lafiya a yankunan har zuwa yau.

Gamayyar ƙungiyoyin matasan Filato da suka haɗa da Afizere, Amo, Anaguta, Atten, Bache, Irigwe, Berom, Buji, Chokobo, Jere, Kurama, Lemoro, Tarya da kuma matasa da mata na ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya reshen jihar, sun yi zanga-zanga a ranar Laraba zuwa gidan gwamnati da ke Jos kan kashe-kashen da ake yi a jihar.

Ƙungiyoyin matasan a wata sanarwa da suka fitar bayan gudanar da zanga-zangar, sun zargi sojojin na Operation SAFE HAVEN da taimakawa wajen taɓarɓarewar tsaro a yankunan da lamarin ya shafa, inda suka ƙara da cewa, ya kamata a xyora musu alhakin kai hare-hare da kashe-kashe a jihar.

Sai dai rundunar a cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Laraba, ta musanta cewa tana da hannu a kisan yayin da ta bayyana zargin a matsayin ƙarya.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labarai na rundunar, Manjo Ishaku Takwa, rundunar ta dage cewa sojojin na Operation SAFE HAVEN sun yi ƙoƙarin daƙile matsalar rikicin ƙabilanci, hare-haren ramuwar gayya da sauran nau’o’in miyagun laifuka a Filato.

Takwa ya ce, “a halin yanzu, shugaban rundunar ‘Operation SAFE HAVEN’ ya damu da tabbatar da zaman lafiya a al’ummomin da suka fuskanci hare-hare kwanan nan a aaramar hukumar Bassa ta jihar Filato da kuma ƙananan hukumomin Zangon Kataf da Jema’a na jihar Kaduna.

“Yadda sojojinmu suka yi gaggawar mayar da martani da shiga tsakani a lokacin waɗannan hare-haren sun daƙile maharan da za su iya cigaba da ayyukansu na ta’addanci ba tare da fuskantar ƙalubale ba. Abin takaici ne yadda aka yi asarar rayuka yayin hare-haren. Muna cikin raɗaɗin duk waɗanda suka rasa ’yan uwansu a hare-haren.

“Daga watan Janairun 2022 zuwa yau kaɗai, Operation SAFE HAVEN ta rasa jami’inta da sojoji 3 a harin ‘yan bindiga. Don haka yana da kyau a lura cewa ƙungiyar ta yi ikirarin cewa Operation SAFE HAVEN ne ke kai hare-haren masu laifi kan al’umma kuma ya kamata a ɗauki alhakin rayukan da aka rasa. Bayanan namu ya kuma nuna cewa, tun daga watan Agustan shekarar 2021, ba a samu hare-haren da aka kai kan al’ummomin ƙananan hukumomin Jos ta Arewa da Kudu, da Barikin Ladi, da Riyom, da kuma Bokkos ba. Masu yin varna suna ƙoƙarin jawo mu baya ne bayan nasarori da dama da aka samu a wuraren da aka ambata.”

Sanarwar ta kuma tabbatar wa gwamnati da ƙaukacin al’ummar ƙasar nan na sadaukarwar da sojojin suke yi na kare rayuka da dukiyoyin duk wani ɗan ƙasa mai bin doka da oda ba tare da tsoro ko fargaba ba.

“A yin haka, muna roƙon jama’a da su ba da sa kai na sahihan bayanai daga ‘yan ƙasar da za su taimaka wajen kama masu aikata laifuka da kuma hana kai hare-hare a kan al’ummarmu.

“Haka nan za mu cigaba da taron masu ruwa da tsaki, taron matasa, tuntuva, da tattaunawa don dakatar da kai hare-hare da ramuwar gayya na dindindin a ƙasarmu,” inji sanarwar.