Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Dakarun Operation Fansan Yamma da na sojojin sama sun gudanar da aikin kakkaɓe maɓoyar ‘yan ta’adda a yankunanan Shinkafi, Kagara, Fakai, Moriki, Maiwa da Chindo a yankin Sokoto da Zamfara yayin da suka hallaka ‘yan ta’adda da dama ciki har da ɗan Bello Turji.
Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau yau Litinin.
Karfin wutar da sojojin suka yi ya haifar da asarar rayukan ‘yan ta’adda da kuma lalata cibiyar haɗa kayan aikinsu.
Sanarwar ta kuma ƙara da cewa, rundunar ta yi nasarar kuɓutar da wasu da Bello Turji ya yi garkuwa da su a yayin samamen.
Sanarwar tayi nuni da cewar Shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji ya tsere ya bar ɗansa da mayaƙan sa a yayin artabun.
Manjo Janar Edward ya ci gaba da cewa, sojojin sun kuma lalata wani sansanin ‘yan ta’adda da aka fi sani da sansanin Idi Mallam a dajin Zango Kagara tare da kashe ‘yan ta’adda 3, tare da kama wasu 3 da ake zargi da haɗa kai dasu.
Sojojin sun kwato bindigu biyu kirar AK47 guda ɗaya da wata kwanson alburusai masu ɗauke da harsashi 11 na alburusai 7.62 mm tare da kwato shanu 61, da tumakai 44 a cikin sauran kayayyaki.
Manjo Janar Edward ya bayyana cewa Sojojin na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’addar Yana mai bayyana cewar Sojojin suna ci gaba da nuna jajircewar su wajen kare dukkan ‘yan ƙasa a duk faɗin yankin arewa maso Yamma.