Sokoto: Za a buɗe kwalejin da aka kashe Deborah

*An umarci ɗaibai su sa hannu kan kundin hana rarzoma

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Watanni biyo bayan rufe Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari kan tarzoma da kisan ɗalibar da ake zarga da yin ɓatanci ga fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAW), mahukuntan kwalejin sun bayyana ranar sake dawo wa karatu.

A zaman da ta yi karo na 79, Hukumar Gudanarwar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari ta amince da sake buɗe kwalejin daga ranar Litinin 8 ga Agustan, 2022.

Deborah

A bayanin da Magatakardan Kwalejin, Malam Gandi Muhammad Asara, ya fitar, ya bayyana buƙatar dake akwai ga dukkanin ɗaliban kwalejin da suke karatun mallakar takardar shaidar malanta ta NCE da ma digiri da su rattaɓa hannu kan wani kundi cewa, ba za su sake tayar da tarzoma a kwalejin ba.

Idan za a iya tunawa, a ranar 13 ga Mayun shekarar nan ne Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ayyana rufe kwalejin, biyo bayan kashe wata ɗaliba da ake zargi da yin vatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW).