Son raƙumin yara

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Karin maganar ta yi dai-dai da abun da za mu yi yau cikin filin mu na koyon tarbiyya. Gaskiyar magana, iyaye mu ƙara miƙewa don ganin mun fitar da yaran mu daga cikin sammatsin rayuwar da muke ciki. Ta wani lokacin sai na dinga ganin mu muke ɓata tarbiyyar yaranmu. Duba da yadda uwa za ta zaƙe wai tilas ita don ɗanta take, bayan cewa kuma ba ta shi take ba. Ta yaya uwa za ta zama ita ce ɗan shi ya zama shi ne uwar? Eh mana uwa za ta zage ita ke bin ɗan bayan ta san shi ɗan shi ya kamata ya bi uwarsa. A yanzu babu wannan, uwa ita za ta yi ta faman yi wa ɗanta bauta da sunan ta fi kowa son sa. Ba ta san kuma sangarta shi take ba, ta kuma kashe masa rayuwa.

Wanki:
Ta yaya uwa za ta ɗebi kayan yaronta ɗan shekaru ashirin da wani abu tana masa wankin? ya Ilahi wannan wacce koyarwa ce ? Shi da zai mata, shi ake yi wa da sunan so ko kuma hidima ta masa yawa. Wannan kam ya wuce so ya koma lalacewa. Idan har uwa za ta yi wa ɗa wankin da ya wuce lokacinsa, to Lallai da sauranmu. Ko Yaron da ya haura shekara goma sha biyu ne, ba za mu yi masa wanki ba. in  in dai a har da lafiyarsa. To shi ya kamata a fahimtar da shi yanayin rayuwa. Mu da iyaye suka koya mana, mun tashi tun muna Shekara goma ake cewa mu wanke Kayanmu. Tun ba sa fita, har ya zame mana jiki. To ta yaya ke uwa da kanki za ki koya wa yaran ki rashin tarbiyya?

Yara mata:
A tunani na na uwa, ana gwada musu wanke -wanke, shara, girki, da sauran ayyuka ƙananan da ba za su gagara ba. Wannan ana yi ne, saboda rayuwar aure. Idan ba su samu a gida ba, to A nan aure na iya gagarar su. A nan za a zo ana samun matsala da surukai ko mazaje. Duk fa daga mu ne iyaye mata!Uwa ta dage da koya wa yaranta ayyukan gidan miji. Ba sai an je, a dinga samun matsala ba.

Girki:
Girki adon mace ne. Duk macen da ba ta samu gogewa a kan wannan fannin ba, to gaskiya da sauranta. Don kuwa daga haka, za ta ɓaro wa kanta tura miji waje cin abinci. Idan mai zurfin ciki ne ma, wallahi ba zai gaya miki damuwarsa ba. Sai dai kawai ki ga kina kwantan abinci. Kuma ki rasa me yasa ba ya cin abinci da kika girka. Idan kin yi ƙwauro na magana ba ki tambaye shi sauyin da kika samu daga gare shi ba, to gagarumin abun da zai miki ɗauko kishiya wacce za ta yi masa abinci. Idan kin hankalta kin gano dalili, shikenan sai ki gyara. Amma kin gama ruguza gidanki da kanki.
Mata da yawa sun raina girki gani suke girki ba wani abu ba ne. Girki kuwa, adon mace ne wata ma da shi take mallake mijinta.

Tsaftar muhalli:
Wannan dai kowacce mace tana da damar da za ta jajircewa kanta wajen tsafta. Ta ɗauki banɗaki, madafi, ɗakin bacci, duk waɗannan abubuwa da na lissafa, yana da kyau mata su mai da hankali kansu. Muddin muka sa lalaci, to kuwa shanyar mu zata jiƙe. Ƙazanta na ɗaya daga cikin nau’in lalata zamantakewar gidanki. Wallahi, kina ji, kina gani, miji zai guje ki. Ƙawaye su sa ki a bakin duniya.

Tsaftar jiki:
Wannan ma zaman kanta take. Kuma ko addini ya yi mana nuni mu yi koyi a kanta. Annabi (SAW) ya ce ” Annazafatu minal imani (tsafta tana daga cikin cikon imani)”.  Don haka kenan tsafta ba abar wasa ba ce. Amma mata da yawa har ma da mazan ba su damu da yi ba. Wanda hakan yana cikin nau’in lalata zamtakewar gidan.Mata Mu kula don Allah mu gyara kawunanmu, da yaranmu.

Yi wa iyayen miji hidima:
Wannan babbar jan martaba ne da ƙarin girmamawa gun miji da danginsa. Idan za ki kula da surukanki tamkar yadda kika kula da iyayenki, to ba shakka kin tsare mutuncinki, da ma na iyayenki. Don komai kika yi, za a ce Koyarwar su ce. Don haka, martaba surukai ba abun wasa ba ne. Koyarwar tarbiyya ce. Kuma yaranki ma, kin koya musu. Saɓanin wasu da suka ɗauki karan tsana suka ɗora wa iyayen mijinsu. Ba su mai da su komai ba face masu yi musu hassada.

Kishiya ba haushi:
Wannan karin magana na jima ina ji gun iyaye. Tun ina tambayar me hakan ke nufi ne? Har na zo na gane ma’anarta. Wato kishi dai wani ciwon zuciya ne a gun mata. Duk wacce aka ce ba ta kishi, na amince ba ta son mijin ko kuma babu tsoka a zuciyarta. Tabbas kishi halak ne, kuma idan yayi yawa haramun. Ba a ce kar ki yi ba, a’a ba mai hanawa. Amma dai ya zama mai tsafta ne ba cutarwa. Irin kishin da muka ji iyaye da kakanni suke yi. Ba na Yanzu ba da ake kisa ko ake ɓata gida ga yara kowanne ɓangare na adawa da ɗaya ɓangaren. Wannan babban kuskure ne, Wallahi.

Wasu iyaye mata ke haddasa wannan matsalar. Wani kuma uba ne da kansa yake rusa rayuwar yaran da matansa, ta fanni daban-daban. Sai yara su tashi da tsanar junansu. Har ta kai matakin da ko buɗe ido ba sa so su yi, su ga junansu. Yanzu wannan rayuwar ake ciki abun ya ƙazanta. Cigaba kullum abun yake. Wanda tsabar kishi ke haddasa haka ɗin. wani kuma soyayyar iyaye ke jawowa an fi son ɗan wani ɗakin fiye da wani. Wallahi mu ji tsoron Allah, mu kyautata rayuwar aure da tarbiyyar yaranmu. Shi kuma uba ya sa ido sosai a kan iyalansa. Ya zamo namijin duniya ba ya tsaya mata na juya shi ba. Muddin zai sa ido sai abun da mata Ko yara suka yi, to ya shirya ganin takaici.

Kyautata tsakanin uba da ’ya’ya:
Ko da ba za a jitu ba, to kar a zurfafa ƙiyayya har yara su gane zaman doya da manjan da ake yi. A nuna musu ƙaunar juna da zumunci. To  har girmansu ko da bayan ran iyaye, to fa babu wanda zai iya raba su. Saboda sun tashi sun ga irin zaman da iyayensu su ke yi.

Ba shi da amfani iyaye na haɗa faɗa tsakanin uba da yaransa. Ko da uban ne mai matsala, idan iyaye mata suka haɗe kansu, wallahi dole ya hakura. Don akwai maza masu haɗa husuma cikin gidansu. Ƙiri-ƙiri gidan sa zai ƙi daɗin zama.

Da yawa maza ke ɓata rayuwar yaransu da matansu. Sai daga baya kuma, ya zo yana da-na- sani. Allah yasa mu dace.

Mu haɗu a sati na gaba.