Soyayyata ga Kwankwaso ta sa ni sauya akalar waƙoƙina zuwa na siyasa – Tijjani Gandu

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ga duk mai bibiyar harkokin siyasa a Nijeriya, musamman abin da ya shafi ɓangaren waƙoƙi, ba zai rasa jin labarin Tijjani Gandu ko waƙoƙinsa, musamman waɗanda yake yi wa jagoran Kwankwasiyya Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ko kuma Bakandamiyarsa ta Abba Gida Gida, da ya yi wa zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf. Ahmad Tijjani Hussaini Gandu kamar yadda cikakken sunansa yake, fitaccen mawaƙin siyasa ne, da ake jin amonsa a duniya ba a Jihar Kano kaɗai ba, saboda salon waƙoƙinsa da yadda yake kwarzanta jagoransa kuma madugun Kwankwasiyya, wanda ya ce yana alfahari da soyayyar da ke tsakanin su, saboda kyawawan ayyukansa da halayensa na jin ƙan talaka. A zantawarsa da wakilin Manhaja, Abba Abubakar Yakubu a Kano, Shugaban Mawaƙan Kwankwasiyyan ya bayyana takaicinsa na yadda ake ɗaukar darajar mawaƙan siyasa da kuma shawararsa ga sabon Gwamnan Jihar Kano.

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka, wanene Tijjani Gandu?

GANDU: To, ni dai asalin sunana Ahmad Tijjani Hussaini, amma an fi sanina da Tijjani Gandu. Ni mutumin Jihar Kano ne daga Ƙaramar Hukumar Birni, wato Kano Municipal. Ni mawaƙi ne kuma ɗan kasuwa. Ni ne shugaban ƙungiyar mawaƙan Kwankwasiyya na ƙasa bakiɗaya.

Ba mu tarihinka a taƙaice.

To, kamar yadda na faɗa ni mutumin Kano ne, haifaffen Ƙaramar Hukumar Birni, a wata unguwa da ake kira Gandun Albasa wacce ke maƙwaftaka da Gidan Adana Dabbobi na Kano. Na fara karatuna daga makarantar allo kafin na shiga firamare da ke nan Gandun Albasa, bayan na gama kuma na shiga Makarantar Sakataren Gwamnati da ke Sharaɗa (GSS Sharaɗa). Daga nan kuma na shiga Kwalejin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano College of Islamic and Legal Studies. Na shiga Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke reshen Kumbotso na wani lokaci, amma ban jima ba karatun ya tsaya saboda wasu dalilai. Mahaifina ɗan kasuwa ne, don haka mu ma muka taso da harkar kasuwanci, a cikinta muka taso kuma har yanzu ana taɓawa, duk da ana taɓa harkar waƙa.

To, yaya aka yi ka samu kanka a harkar waƙa?

Akwai wata sana’a da muke yi a gidanmu, wanda yayana yake yi ta zane zane da sassaɗa abin da ake ce wa wood carving, shi da abokansa da sauran ýan unguwa duk sana’ar da muke yi kenan a lokacin. Muna zana furanni da tsuntsaye, da sauran abubuwa na al’ada. A dalilin wannan aiki ne a kan gayyace ni situdiyo inda ake buga waƙoƙi, ina zuwa zana musu irin abubuwan ado da ake sa wa a cikin ofisoshin waƙa, kamar su kalangu, fiyano da ake kiɗa da ita da sauran su. Yau da gobe muna zuwa aiki muna ganin mawaƙa maza da mata na zuwa yin aikin waƙa, har ni ma na fara sha’awar abin. Watarana sai na ce bari dai ni ma in kwatanta to, wannan shi ne mafari, ga mu nan kuma har yanzu ana bugawa.

A baya an san ka ne a matsayin mawaƙin faɗakarwa, soyayya, da yabon manzon Allah (SAW), sai kuma kwatsam aka ga ka koma waƙoƙin siyasa, musamman waɗanda suka shafi ɗariƙar Kwankwasiyya, ya ya aka yi ka rikiɗe haka?

Wannan soyayya ce ta jawo, don gaskiya ina son madugun Kwankwasiyya Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, ba ni kaɗai ba kusan duk wani mutumin Kano za ka same shi da soyayyar Kwankwaso, saboda yadda ya kawo cigaba a rayuwar jama’a, musamman ɓangaren inganta ilimi, za ka ga ko bai maka ba ya yi wa wani naka. Wannan ce tasa na fara yi masa waƙa, tun ba a sa ni ba. Ka san dai waƙa biya ake yi, kafin a yi to, ni nake sa kaina in yi wa Kwankwaso waƙa don bayyana soyayya ta gareshi. Tun ma babu wanda ya sanni, har Allah ya sa ta fara zuwa kunnen sa, cikin ikon Allah kuma idan na yi waƙar sai a yi sa’a ta yi daɗi. To, a haka dai har Allah ya sa na shiga cikin ƙungiyar mawaƙan Kwankwasiyya, har na zama jami’in watsa labaranta, yau kuma ga shi ni ne shugaba.

Yaya za ka danganta alaƙar ka da jagoran Kwankwasiyya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso?

Jagoranmu ne, ubangidan mu ne, mu kuma yaransa ne. Akwai soyayya mai ƙarfi tsakanin mu da shi, musamman a wannan ƙadamin da ya zama ni ne na gaba gaba cikin mawaƙansa, babu wani mawaƙi da yake waƙe Kwankwaso fiye da ni a yanzu, ban da a baya. Don haka lallai akwai kyakkyawar alaƙa ta kusa tsakanina da Kwankwaso.

Yaya ka ke jin wannan ɗaukaka da Allah ya ba ka ta waƙa a ranka?

To, Alhamdulillahi. Ɗaukaka daga Allah take. Ban taɓa tsammanin waƙa za ta min haka ba gaskiya. Tun da ban shige ta da nufin sana’a ba, a fara waƙoƙina. Sai daga baya ne na ga dacewar in ba ta muhimmanci sosai, har in ɗauke ta daga wannan mataki zuwa wancan, saboda na lura da yadda al’amuran ke tafiya. Ban taɓa tunanin watarana duniya za ta sanni a matsayin fitaccen mawaƙi da ake sha’awar gani ko sauraron waƙoƙinsa ba. Babu abin da nake yi sai yi wa Allah godiya, don kuwa ba wayona ko basirata ko iyawata ba ce. Domin na san akwai dubbanni da suka fi ni iyawa, amma Allah ya ƙaddara ɗaukakar ta wajena. Wallahi har mamakin kaina nake yi, ina tambayar kaina yau ni ne na zama haka?

Ka taɓa zubar da ƙwalla, saboda irin soyayya da ka ke gani daga masoyanka da masu son waƙoƙinka?

Ko da ban zubar da ƙwalla a kan soyayyar da mutane ke nuna min ba, Na sha zubar da hawaye a dalilin waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAW) da na kan yi. Saboda irin baitocin da ake faɗa na soyayya da yabo ga shugaban halitta. Amma a kan soyayya da ake nuna min a karan kaina, sai dai na yi ta ta’ajibi da yi wa Allah godiya.

Za mu ci gaba mako mai zuwa.