SSS ta buƙaci ASUU ta janye yajin aiki saboda matsalar tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A jiya Alhamis ne hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, (ASUU) da ta janye yajin aikin da ta shiga, saboda taɓarɓarewar tsaro.

Daraktan ma’aikata mai kula da jihar Yobe, Yunusa Abdulkadir, ne ya yi wannan roqo a Damaturu a wajen taron kwata-kwata na uku na daraktocin tsaro na jiha a shiyyar Arewa maso Gabas.

Ya ce, yajin aikin da ya gurgunta ilimin jami’o’i a ƙasar, wanda hakan yana da illa ga tsaron ƙasa sakamakon barin matasa a zube babu abin yi.

“Kamar yadda muka san ASUU na bin wata manufa ta gaskiya, ya kamata su yi nazari sosai kan abubuwan da suka shafi yankin Arewa maso Gabas da ya shafe sama da shekaru goma a hannun ‘yan tada ƙayar baya,” inji Mista Yunusa.

Daraktan ya kuma yi kira da a samar da asibitin masu taɓin hankali a Yobe domin duba matsalolin da suka biyo bayan tashe-tashen hankulan da suka faru a baya.

Ya ce rashin yin hakan na iya haifar da munanan raunuka, waɗanda za su iya haifar da wata barazana ta tsaro ga jihar, in ban da na masu tayar da ƙayar baya.

A nasa jawabin, shugaban taron, Hassan Abdullahi ya ce taron zai yi nazari kan barazanar tsaro, da nuna ƙwarewa da kuma tsara hanyoyin da za a bi.

Mista Abdullahi wanda kuma shi ne Daraktan SSS na Jihar Bauchi, ya lissafo matsalolin tsaro a shiyyar da suka haɗa da tashe-tashen hankula, garkuwa da mutane, ‘yan fashi da kuma satar shanu.

Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon baya da haɗin kai ga hukumar SSS da sauran jami’an tsaro.

Mataimakin gwamnan jihar Idi Gubana ya bayyana taron a matsayin wanda ya dace duba da irin ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu.

Ya ce duk da cewa an samu nasarori a yaƙin da ake da ‘yan tada ƙayar bayan, amma akwai buƙatar a ƙara yin aiki don ganin an lalata ragowar ‘yan ta’addan a jihar da kuma yankin baki ɗaya.

Mista Gubana ya ba da tabbacin cewa gwamnatin Gwamna Mai Mala Buni za ta ci gaba da bin manufofinta da manufofin dukkanin hukumomin tsaro a jihar.

Muhimman abubuwan da suka faru a wajen bikin sun haɗa da karramawar da aka baiwa sarakunan Fika da Damaturu, Muhammad Ibn Abali da Shehu Hashimi, bisa rawar da suka taka a yaƙin da ake da ‘yan tada ƙayar baya.