Su waye su ke da alhakin durƙusar da arewa? (I)

Dukkan wani bincike da tarihi, kama daga na jaridu, mujallu, littattafai da dukkan wasu (Documentry) na gidajen Talabijin da Radiyo da suke a ajiye, aka kuma wallafa dangane da tarihin Nijeriya, babban ginshiƙinta shi ne yankin Arewa. Yanki mai cike da albarkatun ƙasar noma da kiwo, ƙoramu da duwatsu haɗi da tafkuna da ake yin noma rani bayan na damuna.

Na daɗe ina rubuce-rubuce a kan al’amurran ƙasata Nijeriya, kuma nasha yin batu a kan ƙalubalen da ke damunta, kama daga batun tattalin arzikin ƙasa, siyasa, ayyukan ta’addanci da taɓarɓarewar al’amurra, wanda kasancewata ɗan ƙasa mai kishi ne yasa nake yin bincike tare da fitowa na faɗi abubuwan da ake yin ba daidai ba, kuma nake fatan a samu sauyi a game da su.

Ina so mu kalli Nijeriya kallo irin na tsanaki domin mu ƙara fahimtar wasu abubuwa, waɗanda duk mai hankali idan ya tsaya ya kalla ya kuma yi nazari, to zai fahimci irin babban ci gaban da Nijeriya ta samu, amma kuma har yanzu ‘yan ƙasar a cikin mawuyacin hali suke. Tsawon shekaru 61 da samun ‘yancin kai daga hannun Turawan Burtaniya, amma har yanzu talakawan ƙasar nan a cikin ƙangin rayuwa suke, mene ne ya jawo hakan? Shi ne, rashin mulkin adalci daga wajen shugabannin siyasa.

A rubuce-rubucena na baya da suka gabata, ga dukkan wanda yake bibiyata a cikin wannan jarida ta Blueprint (Manhaja), ya ci karo da rubutuna da nayi a kan Dimokraɗiyya, wanda na kira da suna: “BABU DIMOKRAƊIYYA A NIJERIA”, wanda na kawo hujjoji da misalai cikin jawabina, don haka ne yasa nake ganin koda Nijeriya taci gaba a tsawon shekaru 61 ko 62 da biyu da samun ‘yancin kai, to ba zai wuce ci gaba irin na masu haƙan Rijiya ba.

Batu na yankin Arewa, dole ne a kira shi da babban yankin da Nijeriya take tunƙaho tare da alfahari dashi, domin shi ne yankin da ake noma abinci, wanda da noman ne ma aka gina ƙasar baki ɗaya. Da albarkatun noma da ake yi a yankin Arewacin Nijeriya aka gina cibiyar wutar lantarki a kudu, aka haƙo mai tare da gina matatun mai a kudu, a ka yi titinan jiragen ƙasa, aka yashe tekuna da samar da cibiyoyin wutar lantarki, a ka kafa kamfanoni da sauransu.

Muna da jihohi 36 a Nijeriya haɗi da babban birnin tarayya Abuja, guda 19 a Arewa, yayin da 15 suke a kudu. Duk wata harka ta kasuwanci Arewacin Nijeriya ne babban jigo kuma cibiyar kasuwa, misali mu ɗauki kamar jihar Kano da take amsa sunan (Center of Commerce) ‘Cibiyar Kasuwanci.’ amma akwai abubuwa da dama da aka durƙusar dasu a jihar, kuma manyan Arewa su ne waɗanda suka yi silar faruwar hakan.

Dalilin da yasa nace Nijeriya ta samu ci gaban mai haƙan Rijiya kuwa shi ne, tun bayan mulkin Abacha al’amurra suka fara rikicewa, ‘yan siyasa suka ɗauki gaɓar lalata ƙasa ta hanyar yin amfani da gurɓatacciyar hanyar hawa kujerar mulki. ‘Yan siyasa irin su Olesigun Obasanjo sun ɗan taka rawa wajen kawo wasu sauye-sauyen cigaban zamani a Nijeriya, kamar wayar hannu ta GSM, ƙananun motocin zamani na sufuri da Bus-Bus, wanda a jihar Katsina lokacin mulkin marigayi Alh. Umar Musa ‘Yar’adua samar da irin motocin KTSTA suka taimaka wajen jigilar fasinjoji a sauƙaƙe, da jihar Kaduna, Kano, Maiduguri, Jos, Sokoto, Bauchi (Yankari), Gombe da sauran jihohi da dama. Wanda a wancan lokacin motocin suna hannun Gwamnatocin jihohin da na ambata, saɓanin da yanzu da mafi akasari suka koma hannun ‘yan kasuwa, kuma yawan motocin ya ragu saboda kasar gwamnati.

Idan muka dawo kan batun manyan jiga-jigan masu kuɗin ƙasar nan ‘yan Arewa ne, manya a siyasa ‘yan Arewa ne, manyan Alƙalai, Jami’an tsaro, Lauyoyi, ‘Yan boko da ‘yan kasuwa duk ‘yan Arewa ne suka fi yawa. Haka nan Malaman Addini, Malaman Makarantu, Likitoci, Injiniyoyi da sauransu duk ‘yan Arewa ne suka fi yawa. Amma yau an wayi gari Arewa tayi faɗuwar baƙar tasa, kimar Arewa ta zube, martaba da darajar Arewacin Nijeriya sun zube. Domin manyan Arewa suna ji kuma suna gani aka ƙirƙiri ƙungiyar ‘yan ta’addan BH (Boko Haram), manyan Arewa suna ji suna gani suka bari aka ƙirƙiri ƙungiyar ‘Kaɗo Wala Nagge’ a jihar Zamfara, daga nan aka sauya su zuwa ‘yan fashin daji, suka koma yin garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa, yau kuma gashi an wayi gari da wasu sabbin ‘yan ta’addar da ake kira (Lakurawa).

Duk wasu abubuwa da suke faruwa na ta’addanci da suka haɗar da; Cin hanci da rashawa, karya doka da oda, satar kuɗin ƙasa, bangar siyasa da ake jefa matasa, fataucin miyagun ƙwayoyi, halasta kuɗin haram, 419 da sauransu, duk waɗannan abubuwan wanne ne manyan Arewa ba su san dashi ba? Suna gani ana yi, wasu ma dasa hannunsu saboda kwaɗayi da rashin jin tsoron Allah, da rashin kishin ƙasa, da kwaɗayin mulki da son tara abin duniya ya rufe musu ido suka bari ƙasa ta lalace, yankin Arewa ya taɓarɓare, ba don ba za su iya hana komai ba da zai lalata yankin suka yi shiru tare da zuba ido ba, sai don kawai su tara abin duniya, su biyawa Turawan Yamma buƙatunsu, yayin da su kuma za su goya musu baya su hau madafun iko.

Babu dalilin da zai sa mu kalli ƙasarmu Nijeriya da yankin Arewa a matsayin ƙasa ko yankin da ya samu ci gaba, domin har yanzu talaka bai san mene ne amfanin Dimokraɗiyya ba, ba ya cin moriyarta. Dalili kuwa shi ne; Bai samu ilimi ingantacce ba, talaka bai samu tsaro ba, bai samu magani a asibiti kyauta ba, balle batun duba lafiyarsa kyauta, hatta da (Paracetamol) sai ya saya da kuɗinsa a asibitin gwamnati. Talakan Nijeriya bai samu wutar lantarki a yankinsa na Arewa ba, babu kyakkyawan yanayi a muhallinsa, babu ingantaccen ruwan sha, bai samu titi mai kyau ba. Duk wata zirga-zirgar talakan Nijeriya yana yinta ne ba a cikin kwanciyar hankali ba saboda rashin tabbas na tsaron lafiyarsa.

Daga shekarar 2009 zuwa yau, babu wasu alƙalumman da za su iya fitar da adadin rayukan da suka salwanta a jihar Borno a sanadiyyar ayyukan ‘yan ƙungiyar boko haram. Ta’addancin da suka yi, yayi sanadin mutuwar miliyoyin mutane, dubbai sun nakasa. An kashe mazaje da dama an bar matansu da marayu, an yi wa dubban mata fyaɗe, wasu sun ɗauki juna biyu sun haifi ‘ya’yan da ubanninsu maza Allah ne kaɗai zai iya sanin mai ɗan ko ‘yar. Duk kuma wannan a Arewacin Nijeriya ya faru. Muna da manyan jami’an tsaro a raye da suka shugabanci ƙasar, da manyan ‘yan siyasa da suka shugabanceta, da manyan Malaman addini da Sarakuna, da manyan attajirai da ‘yan boko, da manyan Alƙalai da Lauyoyi, amma haka aka bar ‘yan boko haram suka yi ta kashe al’umma. ‘Yan siyasa da dama suka fake da wannan suna kushe gwamnati mai ci, suna suka da Allah wadai, ba don son a gyara ba sai don son a ce suna da tausayi da imani tare da kishin ƙasa.

Tabbas! ‘Yan siyasarmu na Arewa suna siyasa ne ba don rayawa ko gina al’ummar yankin Arewa ba, kawai suna yi ne domin gina kansu da iyalansu. Domin ko a lokacin da wannan shugaban ƙasar na yanzu, wato Ahmad Bola Tinubu ya fito neman takarar son zama shugaban ƙasa, manyan Arewa sun goya masa baya ne ba don kishi ƙasa ba, ko don wata kyakkyawar manufa ba, haka nan babu wata rubutacciyar yarjejeniyar wani abu na raya yankin Arewa da suka bijiro masa dashi kuma ya yarda zai yi ba, face kawai ya raba musu maƙudan kuɗaɗe ne suka mara masa ba. Wannan shi yake nuna basu da kishin Arewa, kuma ba ita ce a gabansu ba, illa iyaka su samu kuɗi. Babu ruwansu da makomar talakawa da iyalansu, babu ruwansu da ko me zai faru da Arewa matuƙar za su samu abinda suke so wato (kuɗi).

A lokacin da Tinubu ya tsaya takarar shugaban ƙasa, Haj. Naja’atu Muhammad ta zauna dashi wani lokaci a ƙasar London, ta kuma tambaye shi “Me ya shiryawa Arewa idan ya zamo shugaban ƙasa (don bunƙasa Arewa da ci gabanta)?” amsar da ya bata ita ce, “Ba shi da wani abu a ƙasa na ci gaban Arewa”, ma’ana bai shirya yiwa Arewa wani abun ci gaba ba. Wannan ta faru ne saboda shi yasan su waye ‘yan Arewa, yasan makwaɗaita ne, matuƙar zai sakar musu kuɗi to zai samu goyon bayansu koda zai sayar da Arewar ne gaba ɗaya. Don haka a cikin bayanin da yayi wa Haj. Naja’atu, ya ce idan ya ce zai taɓa manyan Arewa wai za su kashe shi.

Za mu ci gaba a mako a gaba.Daga NAFI’U SALISU. Marubuci/Manazarci, daga Kano Nijeriya. [email protected]@gmail.com. 09056507471-08038981211.