Sufeto-Janar ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin Abba Kyari

Sufeto-Janar na ‘Yan Sandan Nijeriya, IGP Usman Alkali Baba, ya karɓi rahoton kwamitin bincike kan zargin da aka yi wa DCP Abba Kyari na mu’amala da badaƙalar damfara.

Shugaban kwamitin, SIP, DIG Joseph Egbunike, shi ne ya jagoranci miƙa rahoton a babban ofishin ‘yan sanda da ke Abuja ran Alhamis.

Sa’ilin da yake miƙa rahoton, DIG Egbunike ya miƙa godiyarsu ga IGP bisa damar da ya ba su na gudanar da wannan bincike. Tare da cewa, bayan kafa kwamitin a ranar 2 ga Agusta, 2021 ba tare da ɓata lokaci ba ya sunkuya aiki inda ya yi nasarar sauke nauyin da aka ɗora masa kana ya miƙa sakamakonsa kamar yadda aka buƙace shi.

Ya ce rahoton na ɗauke da bayanai da hujjoji da shaidu daga ɓangaren Abba Kyari da sauran ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyin da ke da alaƙa da batun.

IGP ya yaba wa kwamitin da ƙoƙarin da ya yi wajen haɗa rahoton binciken da aka ɗora masa. Ya ci gaba da cewa, an ɗauki matakin yin bincike kan zargin da aka yi wa Kyari ne don bai wa rundunar damar ɗaukar matakin da ya dace.

IGP ya ce za a duba a yi amfani da shawarwarin da kwamitin ya bayar sannan a tura shi ga inda ya dace don ɗaukar matakin da ya dace.

A ƙarshe, IGP ya jaddada ƙudurin rundunarsu wajen tabbatar da adalci a kowane lokaci.

Duka waɗannan bayanai suna ƙunshe ne cikin wata sanarwa wadda ta fito daga hannun mai magana da yawun rundunar na ƙasa, CP Frank Mba, a ran Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *