Sufuri: Gwamna Buni ya ƙaddamar da sabbin motocin bas 20 a Yobe

Daga MUHAMMAD EL-AMEEN a Damaturu 

Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni a ranar Talata ya ƙaddamar da sabbin motoci ƙirar Toyota Hiace masu kujeru 18 guda 20 ga hukumar kula zirga-zurga tare da hukumar kiyaye haɗurra ta YOROTA a jihar.

A jawabin Gwamna Buni a lokacin ƙaddamar da motocin ƙirar bus Damaturu, ya ce taron yar manuniya ce dangane da ƙoƙarin da gwamnatin sa ta tsayu dashi wajen inganta harkokin zirga-zurga don jin daɗin al’ummar jihar Yobe.

Bugu da ƙari kuma ya ƙara da cewa, ”Wannan mataki ne wanda zai ƙara tabbatar da inganta harkokin zirga-zurga tare da lafiyar hanyoyinmu da makamantan su.” 

“Waɗannan motoci ƙirar bus domin hukumar ‘Yobe Line’ mun saya su ne daga kamfanin ‘Westwood Motors Limited’ wanda babu ruwa a ciki, kan Naira miliyan 536, 954, 437.”

Bugu da ƙari kuma, Gwamnna Buni ya miƙa godiyarsa ga kamfanin Westwood Motors bisa haɗakar da ya ƙullla da Gwamnatin jihar Yobe, musamman a daidai lokacin da jihar ke ƙoƙarin farfaɗowa daga matsalar tsaro, kana ya yi kira ga ƙungiyoyin bayar da tallafi su yi koyi da kamfanin.

Haka zalika ya shawarci hukumar kiyaye haɗurra ta YOROTA ta yi amfani da waɗannan motocin wajen faɗakar da jama’a tare da cin gajiyar su a jihar Yobe.

 A jawabin kwamishinan harkokin zirga-zirga da makamashi a jihar Yobe Abdullahi Usman Kukuwa ya yaba da wannan matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *