Sulhu ne samun zaman lafiyar Nijeriya – shugaban hukumar kare haƙƙin ɗan’adam

Daga HARUNA AKARADA a Kano

Ɗaya daga cikin shuwagabannin kare haƙƙin ɗan adam na ƙungiyar nan ta ‘International Human Rights Today’, Kwamred Sa’id Bin Usman. Ya bayyana cewa, sulhu shi ne maslaha a Nijeriya. 

Sa’id ya bayyana haka ne ranar Talatar da ta gabata a yayin  taron manema labarai inda wakilin Manhaja ya samu halarta. 

Shugaban wannan hukumar ta kare haƙƙin ɗan Adam ya bayyana batun da ya fi mai da hankali a kansa wanda shi ne halin da al’umma suka samu kansu a ciki na matsalar tsaro.

Inda ya ƙara da cewa: “Ita aikin hukumar kare haƙƙin ɗan Adam, ta fi maida hankali a kan halin da al’umma suke ciki. Kuma, ita hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ba guda ɗaya ba ce. Aƙalla ta kai kimanin ɗari uku a ƙasar nan. Kuma duk fafukukarsu kare haƙƙin ɗan’adam. Kuma kowanne akwai inda ya fi mai da hankalinsa.

Wasu za ka ga iya kotuna kaɗai, wasu a kan rai kaɗai, wasu kuma a kan ‘yan gudun hijira suka fi ba da ƙarfinsu. Amma mu a wannan ofis, mun fi ba da ƙarfinmu a kan duk wanda aka zalunta, ko wani abu da ya gagari mutane ta fuskar Shari’a, to za mu taka rawa a kan wannan”. Inji shi.

Sannan ya cigaba da cewa: “Duk mutumin da aka zalunta za mu shiga gaba domin ƙwato masa haƙƙinsa. Ko wani ya yi amfani da sarauta ko shugabanci, babu abin da zai gagare mu da ikon Allah. Ko kuma wanda aka ƙwace wa gida ko fili, ko harkar lalata yara, duk wannan hukumar tana bakin ƙoƙarinta don tabbatar da an hukuntasu dai-dai gwargwado.

Ko kuma ka ga matasa sun gama karatu babu abin yi. Wannan ma muna bakin ƙoƙarimmu mu ga komai ya yi dai-dai, mun samar da aiki ga matasan”.

Ya ƙara da cewa, “ko wannan hali da aka shiga ya samu ne sakamakon rashin abin yi ko zalintar wani ɓangare a cikin wannan ƙasa.

Duk fitina wata za ka ji akwai rashin adalci da aka yi wa wasu. Ta gefe guda kuma, wasu tasu fitinar babu dalilin haifar da ita.

A cewar sa, ita hukumar kare haƙƙin ɗan Adam kowa nata ne, idan mun ji an ce ga wasu suna ta’addanci, takan yi ƙoƙarin gano meye ya haifar da wannan ta’addanci, domin a magance, kuma a ceci rawuwar wannan al’umma daga halin da suka samu kansu a ciki.

Domin babu dalilin da za ka magance ‘yan ta’adda ba ka magance dalilin da ya sa suka zama ‘yan ta’adda ba. Don haka, idan al’umna ta rasa abin yi aka ƙuntata mata, takan kauce hanya. 

Akwai wani bafulatani a wani gari shanunsa suka yi ɓarna a gona. Sai aka kama shi aka tsare shanunsa, aka ce sai ya fanshi shanunsa, kuma ba kotu aka kai shi ba. Aka kirawo mahauta aka karyar da shanunsa, aka siyar musu. Ƙarshe dai sai da bafulatanin komai nasa ya ƙare. Kawai sai ga shi cikin ‘yan ta’adda, me gari ya waya? Don haka zalunci yana iya haifar da komai.

Sannan kuma a cewar sa, ko saƙon wasiƙa da wani ɗan ta’adda mai suna Bello Turji ya aika wa masarautar shinkafi da Gwamnan zamfara da shugaban ƙasa,  kira ya yi da a zo a zauna ayi sulhu.

Kuma ya rantse da Allah idan an yi, duk makaman dake wannan dajin zai karɓo ya miƙa wa jami’an tsaro. Wannan hanyar da ya kawo ba mafita ba ce? Mafita ce! To tunda mafita ce, ka ga ya kamata a karɓe ta. Kawai sai ga labari kwatsam an je an afka musu da kisa.

Abin mamakin shi ne, Bello Turji sun daɗe suna cin karensu ba babbaka. Mu tambayar da muke yi, da ma gwamnati tana da ƙarfin maganin wannan ‘yan ta’adda, amma tuni ba’a yi ba sai da suka rubuta cewa a yi sulhu ko kuwa? Akwai masu tsoron idan an zo zaman sulhu asirin wasu zai tonu. 

Wannan kai hari akwai kuskure, dalili: ka je ka samu mutanen da suke ƙoƙarin ajje makami, ka kashe su wanda a da ba ka yi yunƙurin hakan ba. 

Daga nan ɗan gwagwarmayar ya shawarci gwamanati a kan irin matakan da za a ɗauka domin kawo ƙarshe wannan matsala domin kisan ba ya kawo daidaituwa kuma gwamnati ta san kowa nata ne.

Su ma waɗannan mutane masu kisan babu gaira babu dalili, su sani cewa, kisan rai babu dalili Allah ba ya ƙyalewa, don haka su tuba ko Allah ya dube su da rahmarsa. Kuma wannan hukumar kare haƙƙin ɗan Adam ta ji ƙoƙarin da hukumar kwastam ta yi na kama wasu tarin makamai. Wannan gaskiya yunƙuri ne mai kyau, wanda aka gani a Legos shi ya sa muka daɗe muna magana a kan rufe bodar nan dake yankin Nijar.

Har yanzu ba mu tava ji, ko a labarai an ce ga wani makami a wannan guri ba. Don haka gwamnati ta duba kukan mutanan Arewa a buɗe wannan bodar don talakawa su amfana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *