Sunan Alhassan Doguwa ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen waɗanda suka ci zaɓe

Daga BASHIR ISAH

Sunan Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Wakila, Alhassan Ado Doguwa, ya yi ɓatan-dabo daga jerin sunayen ‘yan majalisun da suka lashe zaɓe a zaɓen Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisun tarayya da ya gudana ranar 25 ga Fabrairu.

Wannan na zuwa ne bayan da kotu ta amince ta ba da belin ɗan majalisar wanda ke tsare a kurkuku bisa zargin haddasa rikicin siyasa.

Duk da dai an ayya Alhassan Doguwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen yankinsu, sai dai ba a ga sunansa ba daga jerin sunayen ‘yan takarar da Hukumar INEC ta fitar a ranar Talata waɗanda za ta miƙa musu shaidar lashe zaɓe.

An tsare Alhassan ne kan zarginsa da hannu a rikicin siyasar da ya ci ran wasu mutane da kuma cinna wa ofishin Jam’iyyar NNPP wuta a makon jiya.

Inda daga bisani ‘yan sanda suka gurfanar da shi a gaban Babban Kotun Tarayya a Kano.

Daga bisani, kotun ta amince ta ba fa belinsa kan kuɗi Naira miliyan 500, kana ta haramta masa shiga yankinsu yayin zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a gudanar ranar Asabar, 11 ga Maris.