Sunusi Lamiɗo Sunusi Sarki ne da babu kamarsa: Martani ga Aliyu Ammani a kan rubutunsa ‘soma fiffiken tururuwa’

Daga HARUNA BIRNIWA

Ina farawa da sunan Allah maɗaukakin sarki, tsira da amincinSa su tabbata ga Annabinsa Muhammadu salLahu alaihi wa sallam.

Shi sha’anin Sarki Muhammadu Sanunsi II gobara ce daga kogi, kashe ta sai Allah. Girman Hasada ko tsoron kada Allah Ya yi masa rawani sau biyu har ya cikasa tarihin kakansa Sir, Muhammadu Sanusi (I) da ya mulki Kano kuma ya zama Khalifan Shehu Tijjani ba zai hana Allah yin ikonsa ba. Taɗiya da sare gwuiwoyin mabiya ba zai yi tasiri ba a wannan lokacin, Kano ta numfasa kuma ta amince yave ya fi sabo armashi.

Wai ma ba don tawayar tunani ba ko rashin amfani da tarihi yayin hasashen abun da ka iya afkuwa a gaba, me zai saka dawowar mai martaba, Khalifa Muhammad Sunusi II ya zama barazana ga tarihin sarautun gargajiya? Bibiyar yadda turawan mulkin mallaka suka shigo ƙasar Hausa tare da kafa gwamnatinsu, kana suka zaizayar da ƙarfi da tasirin saurautar a bokonce kaxai ya isa ya gamsar da mai inkarin dawowar tsohon sarkin a karo na biyu cewa ba matsala ba ne. Domin dai da ma gadonsa ne kuma ya taka muhimmiyar rawar da har ila-yau tasirinsa bai dusashe ba a zukatan al’ummarsa, ya taimaka wajen sabunta yanayi da tsarin gudanar da sarautar gargajiya a ƙasar Hausa tun da har ta kai sauran sarakuna yanzu da shi suke koyi.

A yankin da turawa suka zo suka raba sarakuna da baitil-mali, suka maishe su safaya taya ko kuma ‘yan amshin shata waɗanda damar naɗi ko tuɓewarsu ya rataya a wuyan turawa da karnukan farautarsu daga cikin ‘yan siyasa na wancan zamanin duk ba a ce sun lalata tsarin sarautun gargajiya ba sai yanzu da aka tabbatar talakawa sun samu muryar da take iya yin amo da kishinsu?

To mu bar ma zancen kamata ko rashin kamata. Shin idan za a bi ta tsarin shari’a da doka da odar kwansitushin da wanne laifi aka tuve sarkin? Ko kawai don yana takun saqa da gwamnati, ko kuma ya faɗi ra’ayoyinsa kan al’amuran da kowanne ɗan ƙasa yake da ‘yancin magantuwa a gare su? A fahimtar mutane mafi rinjaye, Khalifa Sunusi bai aikata laifin da za a tuɓe shi ba, ka ga kenan dawo da shi gyatta laifi ne ma tabbatar da adalci.

A halin da ake ciki masarautar Kano tana buƙatar madubin kwaikwayo (role model) saboda kasancewarta uwa kuma cibiyar addini da al’ada ta Hausawa, shi kuma samfurin sarki Sanusi irinsa daban ne, duba da zaman sa mutafannini kuma gogaggen ɗan gwagwarmaya wanda furucinsa yake da matuƙar tasiri da daraja a idon duniya, ka ga kenan dawowarsa gidan Dabo ba ƙaramin alheri zai nasar ga sauran jihohi da al’ummatai ba. Irin su ne shugabannin da suke baza naman ƙirjinsu su tarbe harin kibiyar da ya tunkaro mabiyansu. Shi bai ƙi ya yi laifi a idon duniya ba; matuƙar yin laifin ne kaɗai hanyar da zai iya ba wa al’ummarsa cikkakiyar kariya ko da kuwa suna daga cikin masu sukarsa.

Bugu da ƙari, Malam Aliyu, a yadda ka furta maganarka ba tare da ladabi ba kan Sarkin Zazzau sai ya fi kama da zagi fiye da nuna kishin masarautar. Misali inda ka ce “kada ya ɗauka zama ɗan barandar wani ne zai dawwamar da shi a bisa gadon sarautar”, wanda kwata-kwata babu girmamawa a ciki, babu tausasa harshe duk da Annabi Musa ma da Ubangiji (S.W.A) ya aike shi wajen kafiri Fir’auna ce masa ya yi “fa ƙuula lahu ƙaulan layyinan…”

Hakazalika, ka yi sani shi mai arziki ko a Kwara ya sai da ruwa. Ba Zariya ba ko Masarautar Landan ta ƙasar Ingila haka ake yi wa Sarki Khalifa zaman fada, shi sarki ne a halitta haka Rabbu Ya so, ko a hanya ka yi ido biyu ka san kwarjininsa da haskensa ba irin na sarakunan da ka saba gani ba ne.

Ya Allah idan dawowar Sarki cikin fadarsa ce alheri gare shi da al’umma bakiɗaya, ka sauƙaƙa hanyar dawowarsa garemu, idan ko zamansa a gefe zai fi samun kariya da kwanciyar hankali da sauƙin jifan mahassada ka hore masa mu da zukatanmu a matsayin masarautar da zai ta mulki har bayan rayuwarsa.

Haruna Birniwa, marubuci ne kuma mai sharhi a kan al’amurran siyasa. Ya rubuto daga jihar Jigawa.

Lambar waya: 07043759945
Adireshin Imel: [email protected]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *