Suturar mutum uku Aisha ke sakawa saboda ƙiba – Solomon Dalung

Daga BASHIR ISAH

Tsohon Ministan Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Solomon Dalung, ya ce a halin yanzu, suturar da za ta wadaci mutum uku matar Shugaban Ƙasa, Aisha Buhari ke sakawa saboda ƙiba.

Dalung wanda ya riƙe muƙamin Minista a wa’adin farko na Shugaba Buhari, ya faɗi hakan ne a sa’ilin da yake tsokaci dangane da tsare ɗalibi Aminu Mohammed da aka yi don ya soki Aisha Buhari a kafar Tiwita.

Ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da aka yaɗa wanda jaridar Daily Nigeria ta samu gani.

A cewar Ministan, babu abin da ɗalibin da aka kama ɗin ya faɗa face gaskiya.

Ya ce, “A yanzu idan ka kalli Aisha da kyau, za a fahimci ta ƙara ƙiba. Hatta doguwar rigar da take sawa yanzu za ta wadaci mutum uku.

“Ko dai hakan na nuni ba ta da kwanciyar hankali ne kafin wannan lokaci, saboda ba komai take so za ta iya samu ba a wancan lokaci?, inji shi.

Tun bayan kama ɗalibin a Nuwamban da ya gabata, jama’a aka yi ta tofa albarkacin baki, inda wasu ke ganin hakan bai dace ba.

Ana haka ne, sai aka ji Aisha a ranar Juma’a ta janye ƙarar da ta shigar kotu kan ɗalibin, inda lauyanta ya ce ta janye ƙarar ne saboda manyan ƙasa sun saka baki cikin batun.