Taƙaddamar fili: yadda ta kaya tsakanin EFCC da maiɗakin Ganduje

Daga AMINA YUSUF ALI

Hukumar nan mai yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa ta’annnati ta gayyaci Hafsa Abdullahi Ganduje, maiɗakin Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje domin amsa tambayoyi.

Majiyarmu wacce take da alaƙa da gwamnatin Kano, ta rawaito cewa, hukumar EFCC ɗin ta gayyaci maiɗakin gwamnan ne a kan zargin cin hanci da rashawa da suke da alaƙa da wata badaƙalar filaye wadda ɗanta, Abdul-Azeez Ganduje ya shigar a kanta.

Majiyarmu ta ƙara da cewa, EFCC sun sallami Hafsa Ganduje bayan sun shafe awanni suna yi mata tambayoyi. Wato tun safiyar Litinin tana can hukumar EFCC a Abuja. Inda ta sha tambayoyi.

Kuma an bayyana cewa ba ita ta dawo Kano ba sai yau Talata bayan hukumar ta sallame ta tare da umarnin za ta sake dawowa duk sanda hukumar ta sake nemanta.

Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga Satumban shekarar nan jaridar ‘Solacebase’ ta rawaito cewa, hukumar EFCC ta gayyaci matar Ganduje a kan zargin cin hanci da rashawa da ɗanta ya shigar a kanta.

Amma sai ta ƙi zuwa. Har ma hukumar ta ce za ta kama ta, idan ba ta zo ba. Inda ita kuma Hafsa Ganduje ta yi biris da wannan barazanar ta yi tafiyarta ƙasar Ingila wajen bikin kammala karatun ɗanta.