Taƙaitaccen bayani game da matsalar kafa ƙungiyar Hausawa zalla

Daga ABDURRAHMAN ABUBAKAR GUSAU

Gaskiya yau na ƙara fahimtar cewa matsalar arewa ita ce rashin samun wadatatun masana masu rubutu don mutane su gane ba don a gano su ba. Dakta Aliyu U. Tilde lallai cikkaken masani ne da ya kai. Saboda ƙoƙarinsa wajen yin cikkaken bayani a kan wannan matsalar cikin ilimi da hikima.

Sai dai kash! Ba a nan gizo ke saƙar ba, yanzu an riga an baro kyau tun ranar haihuwa. Gaskiya ne a dokar Nijeriya kowa na da ikon kafa ƙungiya don kare martabar ƙabila ko addini. Sai dai wannan Abu da wasu ke yi da sunan Hausawa, a nawa ɗan tunanin, akwai lauje cikin naɗi.

Saboda a ce IPOH ƙungiya mai tsarin suna irin na IPOB ƙungiyar ta’adanci wadda gwammnati ta haramta. Anya ko abinda ake zargi cewa wasu miyagu daga ciki da wajen Nijeriya na da baƙin shiri da tanadi don ganin Arewa ta ruguje ba shi ba ne ko?

Ya dai kamata a tsaya a natsu sosai a yi tunani a kai, jami’an ɓangaren binciken ƙwakwaf da na fikira ‘yan Arewa to ya kamata ku farka ku yo bincike a kan wannan lamari tun wuri. Ni ban taɓa Jin sunan kaltume a cewa sunan Hausawa ne ba duk da yana iya kasancewa.

Na taso ina jin uwayena da kakannina ɓangaren uba suna wasa da fulani a matsayin su na bare-bari ne duk da ko “alanguguro” ban ji suna faɗi ba Hausa dai ce yarenmu. haka ɓangaren mahaifiyata tsatson fulani suna ne kawai ko “walijaam” ban jin suna iya faɗa.

Yanda aka ɓata sunan mutanen Barno da Boko Haram haka aka vata na fulani da ta’adanci. Yanzu kuma ana son kawo wani Abu wai shi ƙabilanci a cikin ƙwaryar Arewa da sunan kare martabar ƙabilar Hausawa daga ta’adancin fulani.
Malamaina Shiekh Abubakar Sodangi Al-gusawiy ga abinda ka daɗe kana faɗa mana ya bayyana a fili. Ana son a ruguza musulmi da musulunci a yankinmu na Arewa ta hanyar laɓewa da sunan ƙabilanci.

Shi dai ɗan ta’adda mutum ne kamar kowa daga kowace ƙabila zai iya fitowa, aikinsa guda ne ta’adanci.

Masu ƙoƙarin kawo ɓaraka a cikin al’ummar Arewa ko dai ‘yan kwangila ne ko masu neman suna don shiga gaba a dama da su a cikin tsarin mugun Shugabanci da ake yi a Nijeriya.

“A dai cigaba da karatu” ta bakin marigayi shiekh Abubakar Mahmud Gummi. Zai fi sauqi. Yohanna Y. D Buru aiki ya karu gare ka domin ga wata sabuwa nan wasu sun vallo. Kukan kurciya jawabi ne!

Abdulrahman Abubakar Gusau
[email protected]
Lambar tarho: 07036119832
© 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *