Ta hanyar haɗa kai ne ‘yan siyasa mata za su samu ‘yancinsu – Fatima Kadashi

“Faɗuwa a siyasa ma nasara ce”

Daga AISHA ASAS

Sanannen abu ne mata a wannan zamani sun yunƙuro kan sha’anin siyasa, sun kuma nuna za su iya idan aka ba su dama ta ɓangaren riƙe madafun iko a ƙasar nan. Sai dai hakan ya zama wata barazana ga wasu mazan ‘yan siyasa ganin cewa idan suka yi wasa hula za ta bi bayan ɗankwali ne a harkar siyasar Nijeriya.

Wannan tunanin na su ne ya sa suke amfani da ƙarfin ikonsu wurin ganin sun hana mata kataɓus a fagen siyasa, ta hanyar danne su, su hana su motsi, har su gaji su gudu don ba inda za su kai kukansu.

A cikin wannan yanayin ne aka samu wata jajirtacciya kuma ƙwarariyya a fagen siyasa da ta kwana ta wuni kan tunanin hanyar sa ma wa mata ‘yancinsu a harkar siyasa tare kuma da ba su wata inuwa da za su iya isa gareta a lokacin da ake ƙoƙarin ganin an sanya su a rana a fagen siyasa.

Hajiya Fatima Abubakar Kadashi jajirtacciyar mace ce da ke ƙoƙarin ganin mata ‘yan siyasa sun zama tsintsiya maɗauri ɗaya don magance tauye haƙƙin da ake yi wa matan da suke fitowa takara. A tattaunawar ta da Blueprint Manhaja, za ku ji irin gudunmawar da ta ke ba wa al’umma da kuma namijn ƙoƙarin da ta yi na kafa ƙungiyar da ta zama mai share kukan matan da suka tsaya takara. Idan kun shirya, Aisha Asas ce tare da Fatima Kadashi:

MANHAJA: Mu fara da jin tarihin rayuwarki.

KADASHI: Assalamu alaikum wa rahmattulla. Ina yi wa masu karatu fatan alheri. Da farko ni dai sunana Fatima Abubakar Kadashi, an haife ni a Kaduna, kuma kusan duk gwagwarmayar karatu na yi shi ne a Kaduna. Na yi firamare a LEA Tudun Wada, sai sakandare da na yi a Maimuna Gwarzo. Daga nan kuma sai na wuce Kaduna Polytechnic na samu difiloma a nan, sannan na wuce Zaria Polytechnic, wato Nuhu Bamali, a nan na yi HND. Sai na sake dawo wa Kaduna Polytechnic don yin digiri na biyu, wanda yanzu haka ina kan yi, Alhamdu lillah. 

Baya ga nan, na yi kwasa-kwasai da dama, kamar na ɓangaren na’ura mai ƙwaƙwalwa da kuma waɗanda na samu na sanin makamar aiki da aka tura mu daga wurin da na yi aiki. 

A ɓangaren karaun addini kuwa, ba abinda zan ce sai dai godiyar Allah, domin an samu daidai gwargwado. 

Kazalika, na yi aiki da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kaduna (KADSIECOM), inda na yi ritaya ta sa kai, wato, ‘voluntary retirement’, ba don komai ba sai don ra’ayin da na ke da shi na yin takara. Bayan haka, Ina da aure, kuma Allah Ya albarkace ni da samun ‘ya’ya uku. Babban shine Aminu, sai Fatima da Yusuf.

Waɗanne ayyuka kika yi a baya?

To, Alhamdu lillah. Ni dai tun asalina ma’abuciya son taimaka wa marasa galihu ce. Asalima zan iya cewa wannan ne ƙashin bayan shigata harkar siyasa, domin da shi na fara. Tun kafin in shiga harkar siyasa na fara harkar tallafi na ƙashin kai, domin na faro daga layinmu, inda na ke ɗan duba marasa ƙarfi, in taimaka masu ta ɓangarori da dama, kamar biyan kuɗin makaranta da sauransu. Ina yi daidai da ɗan ƙarfin da na ke da shi. Daga baya sai na shiga wata ƙungiya mai suna ‘Reality Kingdom’, kuma kusan in ce a lokacin shigata ƙungiyar sai na zama jagaba a harkar. Ayyukan da mu ke yi sun haɗa da: Gyaran maƙabarta, taimakon gajiyayu, kuma mu na zuwa kurkuku mu taimaka wa waɗanda suka samu kansu a ciki bisa kuskure, sakamakon ba su da halin da za su ɗauki ƙwararren lauya da zai kare su. Za mu yi iya mai yi wa don samar masu ‘yancinsu, mu kuma sama masu aikin yi, kamar wankin mota, share-share na ma’aikatu na gwamnati da makamantan su. 

Bayan nan na shiga wata ƙungiyar ta mata wadda yawanci duk matan ‘yan kasuwa ne. To a nan ma dai rawar ba sauya wa ta yi ba, domin harkar taimakon ce dai mu ka ci gaba. Mu na ciyar da marayu, marasa ƙarfi kai har ma da taimakon marasa ƙarfi da ke cikin mu don ganin su ma sun kai ga miƙewa.

Kasancewar na samu ƙwarewa sosai a wannan fage, sai na yanke shawarar buɗe tawa gidauniyar wadda na yi amfani da sunan gidanmu yayin buɗe ta. Wato Kadashi da kike ji ne na yi amfani da shi na buɗe da suna Kadashi Foundation. Ta ƙarƙashin wannan gidauniyar na ke yin ɗan abinda yake ƙarfina ga mabuƙata wanda hakan kan sani farin ciki, kasancewar Ina yin abin da na fi so. Duk da cewa na fi ƙarfi a ɓangaren marayu da kuma matan da mazajensu suka mutu, don a ganina ba wanda ya fi su buƙata.

A daidai wannan gaɓar ce na fara sha’awar harkar siyasa, domin nazari da kuma shawarwarin da mutane ke ba ni, kan cewa, zan iya samun ba wa marayu da zawarawa tallafi fiye da yadda na ke yi a lokacin idan na samu kaina a riƙe ɗaya daga cikin madafun iko.

Yaushe aka kafa wannan ƙungiya da kike shugabanta, wato, ƙungiyar Matan Arewa ‘Yan Takarar Siyasa?

Ita dai wannan ƙungiya ta ƙungiyar Matan Arewa ‘Yan Takarar Siyasa wadda aka yi wa rijista da CAC kamar yadda dokar mallakar ire-iren ta ta tanadar. Mun mata rijista a shekara ta 2018. Kuma na yi mata rijistar ne a lokacin da na fara fitowa takara, ta dalilin fahimtar irin ƙalubalen da mata ke samu a fuskar siyasa. Domin za ki ga lokuta da dama idan mata suka fito takara, aka durƙushe su ko aka nemi su janye da makamantan abubuwan da ake yi wa mata na tauye haƙƙi, sai ki ga gwiwarsu ta yi sanyi, daga nan ba za ki ƙara jin ɗuriyar su ba, saboda ba wata ƙungiya da za ta mara masu baya ko ta zama mai ba su irin taimakon da suke buƙata. To, wannan dalilin ne ya sa na ga tunda ba wanda ya yi, ni bari na yi don amfanin mata ‘yan siyasa waɗanda ke buƙatar irin wannan taimakon.

Da farko dai na fara da nemo mata manyan ‘yan siyasa don su zo ayi tafiyar da su, dama akan ce tafiya da gwani mai daɗi, hakan zai ba wa ƙungiyar damar isa inda ake buƙatar ta je, saboda tana da masana ɓangaren sosai a cikinta.

Alhamdu lillah a shekarar kuwa za mu iya cewa, kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu, domin a shekarar da yake mata da yawa sun fito takara, kuma mun samu mata da yawa daga jihohi da dama da suka yi rijistar da wannan ƙungiyar. Kuma kar ki ce wani aiki ne, ko kashin kuɗi a shiga wannan ƙungiyar. Mu dama burinmu taimaka wa mata ‘yan’uwanmu da suke fagen siyasa, don haka ko ƙwandalla ba ma karɓa da sunan rijista, tun a farkon kafata har ya zuwa yanzu, ba wata mamba tamu da ta taɓa biyan kuɗi wai na shiga ƙungiya. Duk da cewa, ƙungiyar ta fara ƙyanƙyashe manyan ‘yan siyasa mata, hakan bai sa mu ka fara garɓar kuɗin shiga ba. 

Me ya ja ra’ayinki kika kafa wannan ƙungiyar?

To Alhamdu lillah. Abin da ya ja ra’ayina ga kafa wannan ƙungiyar shine, ganin yadda mata ke samun matsaloli a lokacin da suka shiga harkar siyasa, kuma matsalolin na faru da su ne kawai don suna mata. Abu na biyu kuwa, ganin cewa, mu na da mata da suka cancanci su zama shuwagabanni a wani ɓangare, kuma zamansu a muƙaman zai taimaki al’umma, ta sanadiyyar irin hallayansu da kuma baiwa ta iya shugabanci da suke da ita, amma kasancewar siyasa yanzu duk camcantarka idan ba ka da kuɗi wala, don haka rashin kuɗi sai ya hana waɗannan matan kai wa inda za a iya amfana da su, kinga kuwa wannan ci-baya ne gare mu bakiɗaya.

Kamar ni, a lokacin da na yi takara, mijina ne ya ba ni tallafi, ya kuma ƙarfafani fiye da tunani, sai dai ba kowa ne ke da wannan damar da na samu ba. To waɗannan ababe da ma wasu ne suka sa na yi ra’ayin kafa wannan ƙungiyar, don ganin mata sun samu tallafin da suke buƙata.

Menene manufofin wannan tafiyar?

Manufofin ‘Arewa Women Aspirants Forum’ suna da yawa, amma babbar manufar da mu ke da ita ita ce, samar wa mata dama a fagen siyasa kamar yadda maza ke samu ta hanyar amfani da ƙarfinmu, sannaya da kuma ɗan kuɗin da Allah Ya hore mana. Musamman ma ta ɓangaren kuɗi wanda shine kan gaba da komai, kamar yadda na ce sai da su sha’anin siyasa ke yiwa.

Kuma mu na bada taimako ta ɓangaren ilimi kan sha’anin na siyasa, inda za mu haɗa ki da ƙwararru cikin ‘yan ƙungiya da za su dinga sa ki a hanya har a kai ga nasara. Kuma idan ma ba a samu nasarar ba, za mu dinga ƙarfafa miki gwiwa don ganin ba ki fitar da siyasar a ranki ba ko kuma ba ki ce kin daina takara ba. Domin faɗuwa a siyasa ma nasara ce.

Kuma wannan ƙungiya na da shiri na musamman don ƙwato haƙƙin mata da aka yi wa murɗiyar zaɓe. Domin mu na da ƙwararrun lauyoyi da suke shige wa ‘yan ƙungiya gaba don ganin an ƙwato masu haƙƙinsu idan an yi rashin gaskiya a zaɓensu.

Kazalika mu na amfani da sannaya wurin ganin mambobinmu na ko ina da suka fito takara waɗanda ba su samu nasarar ba, mu na bin hanyoyi wurin ganin ba su tashi a hakan ba, ta hanyar bin gwamnatin jihar don samar masu wasu muƙamai a cikinta. 

A matsayinki ta wadda ta taɓa yin takarar zama ‘yar Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna a zaɓen 2019, me za ki ce kan irin matsalolin da mata ke fuskanta a siyasa, musamman a Arewa?

To, alhamdu lillah, duk inda kaga nasara to tabbas sai ka riske ƙalubale. Ita siyasa gaskiya mata suna samun matsala a cikinta fiye da yadda kike tunani. Kuma kar ki ce daga wurin maza kawai, har matan na ba wa mata ‘yan’uwansu matsala. Saboda su mata a komai sai sun saka kishi a ciki. Na samu matsaloli fiye da tunaninki, amma da yake na samu miji mai ra’ayin abin da na ke, shine a kullum yake ƙarfafa min gwiwa kan sanyin da matsaloli suka sa na yi.

Wane irin ƙalubale mata ke fuskanta wajen haɗa aure da shiga harkar siyasa?

Gaskiya akwai ƙalubale masu yawa. Da yawa matan da suka shiga siyasa aurensu na mutuwa ta sanadiyyar, sai waɗanda suka yi sa’ar maza masu fahimta. A kullum na kan gaya wa mata idan mu na ‘meeting’ na ƙungiya cewar, duk wadda ta san mijinta ba ya son ta yi siyasa to ta haƙura da ita, domin shi aure gaba yake da komai. Ban shiga siyasa ba sai da izinin mijina, haka ya kamata kowacce mace ta yi. Bayan haka, idan kina da aure kina siyasa to wallahi sai kin kama kanki, kin yi taka-tsantsan inba haka ba, kina ji kina gani za a lalata miki aurenki ko da kuwa a kan gaskiyarki. Mu kan yi kira sosai kan aji tsoron Allah a tafiyar tare da riƙe darajar aure.

Menene babban abin da ya sa ba a bai wa mata dama sosai a fagen siyasa, musamman a Arewa?

To ai ke Asas ba za su so su ba mu damar ba, saboda suna ganin idan suka ba mu dama za mu zo mu danne su ne. Za ki ga sun yi amanna za ki iya, kuma idan an ba ki dama za ki kawo canji, amma saboda aƙida ta rashin son ganin mata a sama sai su haɗe kai su danne ki ta yadda ba za ki iya motsi ba. Su kuma a Arewa har yau da kufan jahilcin nan na cewa, mata ‘yan siyasa ba kamilallu ba ne, jahilai ne, ba su san cewa zamani ya zo da sauyi a siyasa ba, yanzu sai ma kina da ilimin ne za ki iya samun fage mai kyau a cikinta. Rashin ilimin siyasa ne kan gaba a koma-bayan da mata ‘yan siyasa ke samu a Arewa.

Waɗanne nasarorin ‘Arewa Women Aspirants Forum’ (wato ƙungiyar Matan Arewa ‘Yan Takarar Siyasa) ta samu wajen tallafa wa mata su shiga siyasa har su yi tasiri a ciki?

Alhamdu lillahi! Nasara kam za mu iya cewa an samu daidai gwargwado, domin da farawarmu zuwa yanzu mun samu nasarori masu yawa da in kika yi la’akari da shekarar da mu ka faro, tabbas za a amince mun yi tsalle mai nisa fiye da shekarunmu. ƙaramin misali, S.A wato mai bada shawara ta musamman, mun yi nasarar dasa su a gwamnatoci da yawa, kamar a Kaduna mu na da biyu, a Neja ma haka, ɗaya a Kano, ɗaya a Kogi, ɗaya a Filato kuma mu na da wasu a ‘board members’.

Sai kuma nasarar ƙarfafa wa mata gwiwa don ganin ba su karaya ba bayan faɗuwa. Waɗannan ƙananen misalai ne na irin cigaba da mu ka samu.

Da yawa mata da ke cikin harkar siyasa na ƙorafin maza na amfani da ƙarfin ikonsu wurin hana su cimma nasara kan muƙaman da suka fito takara. Ko kin fuskanci wannan ƙalubalen?

Wannan gaskiya ne. Sau dayawa maza kan yi amfani da ƙarfinsu a siyasa da kuma dukiyar da suke da ita wurin ganin mata ba su kai labari ba a harkar siyasa. Tona masu asiri ne ba ma son mu yi, amma gaskiya suna tauye mata sosai. Idan da akwai adalci to tabbas za ki ga yawaitar mata a madafun iko, saboda suna fito wa takarar kuma ana son su, amma sai kiga maza sun haɗe kai don ganin sun hana haka. Kamata ya yi a jam’iyyu a dinga ba wa mata dama ta musamman saboda mu mu ka fi ƙaranci.

Wane kira za ki yi ga mata da maza a kan shigar matan Arewa harkar siyasa?

Kiran da zan yi na farko dai kan mazan ne, mata aure na da daraja, kuma biyayya ga miji na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar mace, don haka idan miji ya ce, ba ya son siyasa, ki haƙura da ita, zaman aure ma shi kansa siyasar ce. Sai ki yi siyasarki a cikin gidanki, ki samu aljanna. Kai kuwa miji, kafin ka amince wa matarka ta yi siyasa, to dole sai ka bata yarda, kuma sai ka ɗauke kanka. Saboda harka ce ta cuɗanya da maza. Idan ka kula abin da yawa, sai ka ba wa sheɗan damar dasa abin da zai ɓata aurenku.

Mata ku riƙe mutuncin kanku idan mazajenku sun ba ku dama a siyasa. Idan kika kama kanki to duk wani mutumin banza zai ji tsoron matsoki da mummunan zance, don zai fahimci ba shashanci ne ya kawo ki ba. Allah Ya ba mu sa’a.

Mu na godiya.

Ni ma na gode ƙwarai.