Ta kashe ɗanta ta dafa kansa

Wata mata ta kashe ɗanta mai shekara biyar, ta daddatsa sassan jikinsa sannan ta dafa naman kansa ta ci.

’Yan sanda sun cafke matar mai shekara 29 ne bayan sun gano sassan jikin ɗan nata a cikin bokiti a gidanta da ke birnin Faqus a lardin Ash Sharqiyah na ƙasar Masar.

Kafar yaɗa labarai ta Masrawy da ke ƙasar ta ruwaito cewa, maƙure yaron matar ta yi, ta kashe shi sannan ta daddatsa sasan jikinsa.

An ruwaito cewa, kawon mamacin ne ya faro gano abin da ya faru a lokacin da ya ziyarci gidanta, sannan ya sanar da jami’an tsaro.

A ranar Juma’a ’yan sanda sun bayyana cewa matar, mai suna Hanaa ta shaida musu cewa ta dafa kan ɗan nata ta ci ne saboda “tana so ya kasance tare da ita har abada,” ko ya sake komawa mahaifarta.

Hanaa wadda ta aurenta ya daɗe da rabuwa ta shaida wa ’yan sanda cewa ba da gangan ta kashe ɗan nata mai suna Youssef ba, taɓin hankalin da ta ke fama shi ne ya sa ta aikata hakan.

Kafar Masrawy ta ce, an gurfanar da Hanaa a gaban kotu, kuma za a yi mata gwajin kwakwalwa domin tantance lafiyar hankalinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *