Ta raba harshenta biyu don ɗanɗana Pepsi da Koka-kola lokaci guda

Wata mawaƙiya mai suna Brianna Mary Shihadeh mai sha’awar gyaran jiki wadda ta raba harshenta biyu ta bayyana yadda za ta iya ɗanɗana abubuwa biyu daban-daban a lokaci guda.
Hakan dai ya sa mutane suka yi mamakin irin fasaharta wajen bambance ɗanɗano da harshenta da ta raba.

A kwanakin nan ta bar mutane cikin mamaki bayan ta ɗanɗana ruwan lemon biyu a lokaci guda, inda ta sa rabin harshenta a cikin kowane kofin gilashi.

Bayan da aka wallafa bidiyon Brianna Manhajar TikTok wanda ya ɗauki hankalin jama’a sosai, Brianna, wacce ke zaune a Kudancin Jihar Kalifoniya a Amurka, bidiyonta ya samu sharhi da ra’ayoyin mutum 293,000, tare da sanya mabiyanta farin ciki.

A cikin dan lokaci idan an yi la’akari da ra’ayin jama’a game da muhawarar da ɗanɗana lemon Pepsi da Koka-Kola, Brianna ta yi, watakila ya zama abu mai rikitarwa, inda ta tabbatar da cewa, za ta iya ɗanɗana bambanci tsakaninsu lokaci guda.

Brianna – wacce ke da adireshin @flowerfriendly ta gudanar da gwajin ɗanɗanon gishiri da zaki, inda ta raba harshenta a tsakanin gilasan ruwan sukari ɗaya da wani mai ɗauke da ruwan gishiri.

Da ta ke waiwayar irin wannan haɗuwar ɗanɗanon, Brianna ta ce, a bar kwakwalwarta haka ba ta cikin ruɗani. An bar masu amfani da TikTok cikin mamaki bayan sun shaida warewar Brianna da ba kasafai ba ne ake iya samun hakan, wasu sun yaba bidiyonta da cewa ya kasance ‘mai gamsarwa’.

Wani mutum ya ce, “ban tava tunanin yin amfani da wannan ba! Kina da ban-mamaki. Ba zan iya daina kallo ba.”

Wani ya ce, “wannan shi ne abin da na ke buƙata. Tambayoyi da yawa a wannan duniyar kuma babu wanda ke tambayar waɗanda suka dace zuwa yanzu.”

Brianna, wacce wani lokaci ana kiran ta da Flower, tana da fuska mai ado da zanen tattoo da yawa da huda iri-iri a jikinta.