Tabbatar da yanke hukunci don daƙile cin hanci da rashawa a Nijeriya

Hukuncin da aka yanke wa tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Sarah Reng Ochekpe, tare da wasu mutane biyu a baya-bayan nan, wani muhimmin cigaba ne a yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya. Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta kama su ne a ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 a kan tuhume-tuhumen da ake yi masu. Sauran mutane biyun da aka yankewa hukuncin sune Evan Leo Sunday Jitong da Raymond Dabo, waɗanda suka kasance mataimakin darakta a yaƙin neman zaɓen Goodluck/Sambo 2015 da kuma tsohon shugaban riƙo na jam’iyyar PDP a jihar Filato. Ochekpe ya yi aiki a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce, mutanen ukun an same su da laifi tare da yanke musu hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru shida kowannen su daga hannun mai shari’a H. M. Kurya na babbar kotun tarayya da ke Jos a jihar Filato, kan wasu tuhume-tuhume guda uku da aka yi wa kwaskwarima da suka haxa da haɗa baki da kuma karkatar da kuɗaɗe.

Ya ce, “an yi zargin cewa sun karɓi Naira miliyan 450 daga bankin Fidelity ta hanyar tsabar kuɗi da musayar waya da wasu kamfanonin mai da tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke suka yi, don yin tasiri a sakamakon zavien shugaban ƙasa na 2015.

Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa a ranar 26 ga Maris, 2015, babban bankin Fidelity reshen Jos, ya cire kuɗi Naira miliyan 450 daga babban bankin Nijeriya, aka miƙa wa waɗanda ake tuhuma a cikin tsavar kuɗi bayan sun sanya hannu don karɓa. Duk da cewa waɗanda ake tuhumar sun yi ikirarin cewa sun miƙa kuɗin ne ga marigayi Sanata Gyang Pwajok, ɗan takarar gwamnan jihar Filato a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2015, amma ba su iya bayar da wata shaida da za ta tabbatar da ikirarin nasu ba.

Ƙidaya ɗaya daga cikin tuhume-tuhumen da ke cewa a wani ɓangare, “wani lokaci a cikin watan Maris 2015 a Jos, Jihar Filato ta Nijeriya da ke ƙarƙashin ikon wannan kotun mai girma, ba tare da bin ƙa’idar kuɗi ba, kun haɗa baki a tsakanin ku don karɓar kuɗi daga Naira miliyan ɗari huɗu da hamsin (N450,000,000) daga wani Annet Olije Gyen, shugabar ayyuka na bankin Fidelity reshen Jos wanda adadin ya zarce adadin da doka ta tanada kuma ta aikata laifin da ya saɓawa tanadin sashe na 18 (a). Sashe na 16 (1) (d) na Dokar Hana Kuɗi (Haramta) ta 2012 (kamar yadda aka gyara) kuma mai hukunci a ƙarƙashin sashe na 16 (2) (b) na wannan dokar.

Yayin da aka yanke wa waɗanda ake tuhuma hukunci a kan ƙirga na ɗaya, wanda ke da alaqa da haɗa baki wajen karɓar kuɗi sama kima a ƙarƙashin dokar haramta safarar kuɗaɗen haram ta shekarar 2012 (kamar yadda aka yi wa kwaskwarima) hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari tare da zaɓin tarar N2,000,000 (Naira miliyan biyu). kowannen su an same su da laifuka biyu da kuma yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru uku a gidan yari tare da zaɓin naira miliyan biyu (N2,000,000) kowanne.

Za a gudanar da hukunce-hukuncen a jere. Sai dai kotun ta sallame su tare da wanke su a kan wasu laifuka uku da ke da iyaka da tsare wasu kuɗaɗe.

Hukuncin da aka yanke wa Sarah Ochekpe da wasu mutane biyu bisa zargin haɗa baki da halasta kuɗaɗen haram wani cigaba ne mai kyau da ya kamata ya hana jami’an gwamnati cin mutuncin mukamai. Har yanzu babban abin koyi ne ko da jami’in gwamnati da aka yanke wa hukunci ya zavi zacin biyan tara fiye da ɗaurin kurkuku. Aƙalla, kunya za ta kasance tare da su har abada abadin. Labarin da aka buga na kasancewarsu waɗanda ake tuhuma a shari’ar cin hanci da rashawa ya isa abin kunya ga kowa, ballatana wanda ta tava riƙe muƙamin minista a Tarayyar Nijeriya.

Wannan wulaƙanci ya yi muni da zai hana kowa yin amfani da duk wata damarmaki da za ta same su a gaba wato idan sun yi. Haƙiƙa wannan ya zama darasi ga sauran jami’an gwamnati da ke da hannu wajen aikata almundahana ko wasu ayyukan da ba su dace da al’umma ba, cewa wata rana doka za ta riske su.

Blueprint Manhaja na kira ga EFCC da ta bi duk wasu da aka tuhume su da laifin cin hanci da rashawa domin ganin an gurfanar da su a a gaban kotu. Sai dai duk da haka, tsawon lokacin da EFCC ta ɗauka na tabbatar da hukunta waɗanda ake tuhuma a wannan shari’a, kamar sauran mutane, abu ne da ke damun su.

Lauyoyin masu shigar da ƙara na EFCC da sauran hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa a ƙasar nan suna ƙarfafa su shirya tare da gurfanar da waɗanda ake tuhuma ta hanyar da za ta gaggauta shari’a.

Wannan yana buƙatar cikakken bincike, ingantaccen tuhume-tuhumen da gabatar da dabarun gabatar da shaidu. Idan aka yi la’akari da girman lamuran cin hanci da rashawa da aka ruwaito a kafafen yaɗa labarai, yawan muatnen da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa suka kama ya yi ƙasa da tsammanin jama’a. Wasu jami’an gwamnati da aka yankewa hukunci a baya sun haɗa da tsohon gwamna Joshua Dariye, tsohon gwamna Jolly Nyame da Farouk Lawan, tsohon ɗan majalisar wakilai.

A yayin da muke kira ga gwamnati da ta janye duk wani ɗaga ƙafar da ta ke yi wa jami’an gwamnatin da aka samu da laifin cin hanci da rashawa, muna ba da shawarar cewa a yi cikakken bincike kafin a ci gaba da bayar da irin waɗannan karamcin.

Dole ne jami’an gwamnati su yi biyayya ga dokokin kuɗi kuma su daina cin zarafin jama’a da sace kuɗaɗen ƙasa.